Umarni daga Kotu zuwa ga EFCC, DSS, da ‘Yan sanda: Kada ku sake ku bincika gidan Gwamnan Rivers

Umarni daga Kotu zuwa ga EFCC, DSS, da ‘Yan sanda: Kada ku sake ku bincika gidan Gwamnan Rivers

- Gwamnan jihar Rivers ya samu nasarar hana hukumomin tsaro bincika gidajensa

- Nasarar tasa ta biyo bayan karar da ya shigar gaban kotu yana mai kalubalantarsu bisa rashin hurumin yin hakan domin kariyar da kundin tsarin mulki ya bashi a matsayinsa na Gwamna

Wata babbar Kotu mai zamanta a Abuja ta dakatar da duk wani yunkuri da hukumar EFCC da DSS da kuma Rundunar ‘Yan sanda yi na caje gidan gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike.

Umarni daga Kotu zuwa ga EFCC, DSS, da ‘Yan sanda: Kada ku sake ku caje gidan Gwamnan Rivers
Umarni daga Kotu zuwa ga EFCC, DSS, da ‘Yan sanda: Kada ku sake ku caje gidan Gwamnan Rivers

Gwamnan dai ya garzaya kotu ne tun shakarar da ta gabata (2017) don neman kotun ta dakatar da takardar neman izinin caje gidansa da suke nama.

Da yake yanke hukunci kan maganar a yau Laraba, mai shari’a Ahmed Mohammed ya ce ya yanke hukuncin ne bisa dogaro da sashi na 308 da 149 da 150 na kundin tsarin mulkin kasar nan ya yi hani ga duk wata tuhuma da za’a yiwa gwamnan.

KU KARANTA: Cikin hawaye da alhini: An yi jana’izar Faladinawa fiye da 50 da Sojin Isra’ila suka yiwa kisan gilla (Hotuna)

Sannan ya kara da cewa, bisa kariyar da doka ta ba shi babu yadda za’ai yana kan kujerar gwamna mai ci ayi karar a bisa umarnin sashi nan 308(1)(c).

Alkalin ya kuma ce babu yadda za’a ai hukumomin tsaron su caje gidan gwaman alhali yana kan mulki ko da kuwa baya cikin gidan nasa, kamar yadda sashin kundin tsarin mulki ya fada saboda kar a dauke musu hankali wajen gudanar da mulkin al’umma.

A dalilin hakan ne mai shari’ar ya ja hankalin hukumomin da akul dinsu suka sake suka caje gidan gwamnan a ko ina yake ba lallai sai gidansa na Abuja ba mutukar gidan a Najeriya yake.

Manema labarai sun rawaito cewa, gwamnan ya shigar da karar ne ta hannun lauyansa Sylva Ogwemoh (SAN), a watan Yuli na 2017 bisa dogaro da sashi na 308 da ya bawa gwamnan kariya har sai ya sauka daga mulki. Amma kuma wadanda ake karar (EFCC,DSS,NPF) sun dage da cewa tabbas suna da hurumin bincikar gidan na gwamnan mutukar baya cikinsa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel