Wa ya aike ka? – Fadar shugaban kasa ta caccaki jakadan Najeriya da ya halarci taron bude ofishin jakadancin Amurka a Birnin Kudus
Gwamnatin tarayya ta caccaki jakadan Najeriya zuwa Isra’ila da halarci taron bikin bude ofishin jakadancin kasar Amurka a birnin kudus duk da cewa manyan kasashen duniya sun nuna rashin amincewansu da hakan.
Wani jami’in fadar shugaban kasa a daren jiya Talata ya bayyanawa manema labarai cewa ministan harkokin wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama, ya caccaki jakadan.
Mayar da ofishin jakadancin Amurka birnin Kudus daga Tel Aviv ya fusata Falasdinawa kuma akalla guda 60 sun rasa rayukansu.
Fadar shugaban kasa ta ce Najeriya bata halarci taron ba kamar yadda Al Jazeera ya ruwaito.
Jami’in fadar shugaban kasa wanda aka sakaye sunansa ya ce gwamnatin tarayya ta bukaci AlJazeera ta janye magananta cewa Najeriya ta halarci taron.
KU KARANTA: Anyi kira ga Magu da kada ya saurarawa Barayi
Yace: “Bisa ga rahoton, ministan ya caccaki jakadan yayi bayanin dalilin da yasa ya halarci taron. Jakadan ya musanta hakana”
“Bisa ga hakan ne gwamnatin tarayya ta bukaci Al Jazerea ta janye labarin.”
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng