Kasar Jamus zata dawo da ‘yan Najeriya 30,000 wadanda suke kasar ba bisa ka’ida ba

Kasar Jamus zata dawo da ‘yan Najeriya 30,000 wadanda suke kasar ba bisa ka’ida ba

- Kasar Jamus ta kawo shawarar mayar da ‘yan Najeriya da suke a cikin kasar ba bisa ka’ida ba a kalla 30,000 zuwa gida Najeriya

- Ministan al’amuran kasar waje, Geoffrey Onyeama ya bayyana hakan lokacin da ya karbi bakuncin mai bawa shugaban kasar Jamus shawara ta fannin tsaro, Dr. Jan hecker da jama’arsa a birnin tarayya

- Gwamnatin kasar ta Jamus ta kawo shawarar ne bayan ta fahimci cewa wannan gwamnatin ta kasa tabbatar da cewa mutanen kasar basa fita daga kasar ba bisa ka’ida ba

Kasar Jamus ta kawo shawarar mayar da ‘yan Najeriya da suke a cikin kasar ba bisa ka’ida ba a kalla 30,000 zuwa gida Najeriya.

Ministan al’amuran kasar waje, Geoffrey Onyeama ya bayyana hakan lokacin da ya karbi bakuncin mai bawa shugaban kasar Jamus shawara ta fannin tsaro, Dr. Jan hecker da jama’arsa a birnin tarayya.

Yace Gwamnatin kasar ta Germany ta kawo shawarar ne bayan ta fahimci cewa wannan gwamnatin ta kasa tabbatar da cewa mutanen kasar basa fita daga kasar ba bisa ka’ida ba.

Kasar Jamus zata dawo da ‘yan Najeriya 30,000 wadanda suke kasar ba bisa ka’ida ba
Kasar Jamus zata dawo da ‘yan Najeriya 30,000 wadanda suke kasar ba bisa ka’ida ba

Inda ya kara da cewa a shekarar data gabata mutane 200 kadai ne suka dawo gida Najeriya a cikin mutanen 30,000 da suke a kasar ta Germnay ba bisa ka’ida ba.

KU KARANTA KUMA: An gano shugaba Buhari a kasuwa tare da gwamnan jihar Jigawa (hoto)

Jack Hecker yace yazo kasar Najeriya ne domin kulla zumunta ta kirki a tsakanin kasar ta Germany ta Najeriya don samun mafita ga matsalar data shiga tsakani musamman ta fannin ‘yan gudun hijira.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel