Kilu ta jabau: An yankewa dan warcan jaka wata 6 a kurkuku

Kilu ta jabau: An yankewa dan warcan jaka wata 6 a kurkuku

- Dubun wani barawon mai kwacen jakar Mata ta cika

- Hary alkali ya sanya a ingiza keyarsa gidan Maza ko ya biya tara

Alkalin wata kotu a Abuja Abubakar Sadiq, ya yankewa wani mai warcewa Mutane jakkunansu Chukwuemeka Ndukwu hukuncin watanni shida a gidan yari yau Talata.

Yanke hukuncin dai ya biyo bayan bayan da Chukwuemeka Ndukwu ya amsa aikata laifuka biyu da ake zarginsa da shi; Sata da kuma kwace.

Kilu ta jabau: An yankewa dan warcan jaka wata 6 a kurkuku
Kilu ta jabau: An yankewa dan warcan jaka wata 6 a kurkuku

Mai shari’a Sadiq ya ba wanda ake zargi zabin hukuncin biyan tara ta Naira 20,000.

KU KARANTA: Hazikin dan sanda Abba Kyari ya samu karin girma (hotuna)

Tun da fari dai ‘Dan sanda mai gabatar da kara Dalhatu Zannah, ya shaidawa kotun cewa a ranar 28 jama’an sintiri na rundunar ‘yan sanda dake yankin Utako suka cafke wanda ake zargin mai shekaru 37, da misalin karfe 10:50pm na dare a wata maboyar masu laifi.

Zanna ya ce, wadanda ake zargin da yaransa suna labewa a mafakar tasu su rika yiwa Mata kwacen jakarsu da wayoyi da sauran abubuwan amfani. Kuma tun a yayin tambayoyi wanda ake zargin ya shaidawa ‘yan sandan lallai ya aikata laifin.

Wanann laifi ne da ya ci karo da sashi na 79 da na 29 na kundin tsarin mulki. a cewar jami'in.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng