Ganduje zai kashe Miliyan 345 don ciyarwa a watan Ramadan

Ganduje zai kashe Miliyan 345 don ciyarwa a watan Ramadan

- Gwamnan Kano zai gwangwaje masu karamin karfi a watan Ramadan

- Za'a na girka abincin buda baki ana rabawa kyauta ga masu Azumin

Gwamnatin Kano ta shirya tsaf don kashe Naira Miliyan N345 domin ciyarwa a watan Ramadan na wannan shekara.

Kwamishinan yada labarai, Matasa da al’adu kuma shugaban kwamitin ciyarwar na watan Azumin bana, Malam Muhammad Garba ne ya tabatar da hakan yayin kaddamar da shirin ciyarwar a harabar madaba’ar jihar.

Ganduje zai kashe Miliyan 345 don ciyarwa a watan Ramadan
Ganduje zai kashe Miliyan 345 don ciyarwa a watan Ramadan

Muhammad Garba ya jaddada cewa gwamnatin Gandujen ta dora ne akan kyakkyawar dabi’ar ciyarwar ga ma su karamin karfi a jihar a watan na Azumi.

Kuma kwamitin da yake jagoranta ne zasu saka ido wajen ganin an gudanar da tsarin yadda ya kamata.

Garba ya ja kunnen wadanda aka baiwa kwangilar dafa abincin da su tabbatar da inganci da tsaftar abincin nasu, domin kwamitin nasa bazai yi kasa a gwuiwa ba wajen maganin duk masu yunkurin kawo wa shirin matsala.

KU KARANTA: Aiki ga mai kareka: Buratai ya bawa Sojoji wa’adin makwanni 3 su gama da ‘yan tada kayar baya a Birnin Gwari

Daga nan ne yayi kira ga masu hannu da shuni da su rungumi dabi’ar ciyarwar ta hanyar tallafawa kokarin gwamnatin don tabbatuwar tsarin.

Kana ya lissafa abubuwan da aka rarraba ga cibiyoyin girka abincin goman farko na Azumin daga cikin akwai; Buhu 3,000 na Shinkafa da 1,170 na Gero da 780 na Fulawa da 1,170 na Sukari da katan din Taliya 1,950 da jarkar Man gyada guda 2,340 da 780 na Manja da kuma buhun Dabino 390.

Sannan kuma za’a rika bayar da Naira 10,000 kullum ga kowacce cibiyar kirkin a kullum domin siyan kayan girkin har Azumin ya kare.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel