Allah ya tsinewa wadanda suke yiwa Falasdinawa kisan kiyashi
Shugaban kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdoğan ya yi tofin Allah tsine akan masu aikata kisan gilla ga al'umar Falasdinawa da kuma wadanda suke kallon irin wannan zaluncin batare da sunce komai ba
Shugaban kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdoğan ya yi tofin Allah tsine akan masu aikata kisan gilla ga al'umar Falasdinawa da kuma wadanda suke kallon irin wannan zaluncin batare da sunce komai ba.
DUBA WANNAN: Zamu rarrabawa ‘yan Najeriya kudaden da Abacha ya sata – Shugaba Buhari
Shugaban kasar na Turkiyya wanda ya kai ziyara kasar Ingila yayi maganar ne a lokacin da yake ganawa da daliban kasar sa da suke karatu a kasar ta Ingila.
Erdoğan wanda ya soki kisan da kasar Isra'ila ta yiwa Falasdinawa da dama a daidai lokacin da kasar Amurka ta maida ofishin jakadancinta daga Tel Aviv zuwa binin Qudus.
Shugaban yace, "Kasar Isra'ila tana aikata ta'addanci. Sannan kuma kasar Isra'ila kasar ta'addanci ce. Saboda haka kasar Turkiyya zata cigaba da kasancewa tare da al'ummar Falasdinawa"
Shugaba Erdoğan yace,
"Abinda kasar Isra'ila keyi kisan gilla ne. Muna la'antar afkuwar wannan kisan kiyashi da ake yiwa Falasdinawa koda kuwa daga wace kasa zaluncin ya fito, daga Amurka ko kuma Isra'ila".
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng