A nemi wata ranan Laraba – Sarkin Musulmi

A nemi wata ranan Laraba – Sarkin Musulmi

Mai alfarma Sarkin Musulmi kuma shugaban majalisar al’amurorin sharia ta koli, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar, yayi kira ga daukacin al’umma Musulmi su nemi watan Ramdana ranan Laraba, 15 ga watan Mayu, 2018.

Mataimakin sakataren NSCIA, Farfesa Salisu Shehu, a wani jawabi da ya saki yau yace mai alfarma sarkin Musulmi yana taya daukacin al’umma murnan gabatowan watan Ramadana. Yana kira ga al’umma suyi amfani da wannan wata domin neman ni’imomin Allah.

KU KARANTA: Dakarun sojin Najeriya sun kashe mayakan Boko Haram biyu yayin kubutar da wani tsoho

Bisa da shawaran kwamitin gani wata na kasa, Sarkin Musulmi yayi kira ga al’umman Musulmi su nemi watan Ramadanan 1439 da yammacin ranan Laraba, 16 ga watan Mayu 2018 wanda yayi daidai 29 ga watan Sha’aban.

Idan Musulmi amintacce ya ga wata da yammacin gobe. Mai alfarma zai sanar da Alhamis, 17 ga wtaan Mayu 2018 a matsayin ranan 1 ga watan Ramadana.”

“ Amma idan ba’a ga wata ba a ranan, za’a tashi da azumi ranan Juma’a, 18 ga watan Mayu, 2018. Majalisa na kira ga Musulmi a fadin kasa su saurari sanarwan mai alfarma domin fara azumi,”

Bugu da kar, za’a iya tuntuban mambobin kwamitin duba wata ta kasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel