Ana gwarama: Ina da ‘ya’ya 19 da mata goma suka Haifa min ba tare da na aure su ba, wani mutum ya shaidawa kotu

Ana gwarama: Ina da ‘ya’ya 19 da mata goma suka Haifa min ba tare da na aure su ba, wani mutum ya shaidawa kotu

- Abin da mamaki Karuwai su haifawa Mutum har 'ya'ya 19 ba tare da ya auri ko guda daga cikinsu

- Irin wannan badakala ce ta faru da wani Mutum a kasar Kenya

- Iyalan Matarsa bayan ta mutu suka hana shi halartar bikin binne ta, inda shi kuma ya kalubalance su a kotu kuma yayi nasara

Wani tsohon jami'in kula da harkokin kudi a kasar Kenya ya musanta zargin da iyalan tsohowar matarsa ke masa na cewa ya auri mata har guda 10 bayan rabuwarsa da 'yar uwarsu shekaru 17 da suka wuce.

Ana gwarama: Ina da ‘ya’ya 19 da mata goma suka Haifa min ba tare da na aure su ba, wani mutum ya shaidawa kotu
Ana gwarama: Ina da ‘ya’ya 19 da mata goma suka Haifa min ba tare da na aure su ba, wani mutum ya shaidawa kotu

Mutumin mai suna James Matele Weindaba da kuma iyalan Beatrice Nyongesa sun gurfana a gaban wata kotu domin sanin wa ke da 'yancin binne ta bayan rasuwarta.

Beatrice wadda tsohuwar malamar gaba da sakandire ce ta Kitale Polytechnic dake kenya, sun yi aure da James har na tsawon shekaru 3 inda suka samu yara 3, kafin daga bisani ta kamu da cutar kansar nono (breast cancer) wanda ta zamo ajalinta daga karshe.

KU KARANTA: Rundunar Yansanda ta fara binciken kwakwaf kan ayyukan matsafa a jihar Borno

Iyayen Beatrice sun bayyanawa kotu cewa, James ba shi da hurumin binne mamaciyar saboda ya auri mata daban-daban har guda 10 tare da 'ya'ya har 18. Suka kara da cewa dama tun asali lokacin da auresu bai cika duk wasu al'adu da ake yi kafin aure ba, wanda ya hada da kayan aure da kuma kudin sadaki, don haka suna neman kotu ta basu izinin binne ta.

Daga bisani bayan duban tsanaki akan lamarin tare da nemo wasu bayanai ta bawa James damar ganin gawar matar tasa da kuma ba shi izinin binne ta, sabanin hana shi ganin gawar da iyalanta suka yi da farko a lokacin da aka ajiyeta a dakin ajiye gawawwaki, wannan hukunci dai an zartar da shi ne bisa umarnin alkali Anne Makau.

Daga karshe James ya dauki gawar matar tasa inda ya samu halarta tare da taimakon 'yan uwansa wajen binne ta a kauyen Mabuye dake can hanyar Lugari a kasar ta Kenya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng