Yanzu Yanzu: Yan shi’a dake zanga-zanga sun kora jami’an yan sanda a Abuja

Yanzu Yanzu: Yan shi’a dake zanga-zanga sun kora jami’an yan sanda a Abuja

Matasan kungiyar Musulman Shi’a zanga-zanga kan cigaba da tsare shugabansu, Ibrahim El-Zakzaky, da gwamnatin Najeriya keyi sun mamaye harabar sakatariyar tarayya, Abuja, sannan kuma sun mamaye hanyoyin dake yankin.

Babu nisa tsakanin harabar sakatariyan da majalisar dokoki da kuma fadar shugaban kasa.

Matasan wadanda ke rike da manyan suwatsu sun tarwatsa tawagar yan sanda sanna kuma suka juya abun dake bayar da hannu don hana cunkoso dake hanyar.

Yanzu Yanzu: Yan shi’a dake zanga-zanga sun kora jami’an yan sanda a Abuja
Yanzu Yanzu: Yan shi’a dake zanga-zanga sun kora jami’an yan sanda a Abuja

An rahoto cewa sun raunata jami’in dan sanda na sakatariyar tarayyan a fuska bayan ya bukaci su daina ci zarafin masu motoci.

KU KARANTA KUMA: Zan karbi shawarar sauke ni da farin ciki – Kakakin majalisar jihar Kano

Sun ja a yan sanda kan cewa idan sun isa su hanasu aiwatar da zanga-zangarsu yayinda suke wakar “a saki El-Zakzaky”.

Wannan dai ba shine karo na farko da yan shi'an ke karawa da yan sanda ba, a baya Legit.ng ta ruwaito cewa yan sanda sunyi amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa masu zanga-zangan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng