An kama mutane 6 bayan sunyi walankeduwa da gidan sauro 6,000 a Kebbi

An kama mutane 6 bayan sunyi walankeduwa da gidan sauro 6,000 a Kebbi

- Manyan motoci biyu da akayi amfani dasu wurin yanke hanya da gidan sauro 6,000 sannan kuma sai mutane 6 aka kama a garin Jega

- Gidajen sauron wadanda kungiyar bayar da tallafi ta fannin kiwon lafiya (WHO) suka bayar, an yanke hanya dasu zuwa jihar Kano da Jigawa kafin ‘Yan Sanda suka kamasu

- Jami’in ‘Yan Sanda mai kula da harkokin jama’a DSP Mustapha Sulaiman yace mutane mutanen shida da aka kama da laifin satar gidajen sauron an mikasu zuwa CID don cigaba da bincike

Manyan motoci biyu da akayi amfani dasu wurin yanke hanya da gidan sauro 6,000 sannan kuma sai mutane 6 aka kama a garin Jega dake jihar Kebbi.

Gidajen sauron wadanda kungiyar bayar da tallafi ta fannin kiwon lafiya (WHO) suka bayar, an yanke hanya dasu zuwa jihar Kano da Jigawa kafin ‘Yan Sanda suka kamasu.

Wakilin kungiyar ta kula da bayar da tallafi ta fannin lafiya wato WHO, Mr. Sam Olaremu, ya bayyana rashin jin dadinsu game da al’amarin.

An kama mutane 6 bayan sunyi walankeduwa da gidan sauro 6,000 a Kebbi
An kama mutane 6 bayan sunyi walankeduwa da gidan sauro 6,000 a Kebbi

Kwamishinan lafiya na jihar Alhaji Umar Usman Kambaza, yace ana nan ana gudanar da bincike saboda haka ma’aikatar bazata iya cewa komai ba har sai an gama gudanar da binciken.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya isa jihar Jigawa (hotuna)

Jami’in ‘Yan Sanda mai kula da harkokin jama’a (PPRO) DSP Mustapha Sulaiman yace mutane mutanen shida da aka kama da laifin satar gidajen sauron an mikasu zuwa CID don cigaba da bincike.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel