Ikon Alah! Ya bada sadakan fili ga makabarta ranan Asabar, ya rasu da daddare, shi aka fara birnewa a filin

Ikon Alah! Ya bada sadakan fili ga makabarta ranan Asabar, ya rasu da daddare, shi aka fara birnewa a filin

Wani rahoto da jaridar Legit.ng ta samu rahoton rasuwa wani bawan Allah wanda ya sayi fili ranan Asabar, 12 ga watan Mayu, 2018 ya baiwa makabarta kyauta FisabiliLlahi.

Bayan mutumin mai suna Alhaji Ali Tela da ke zaune a Lagos Street ya bada wannan fili, Allah ya dauki ransa da daren ranan kuma an birnesa da safiyar ranan Lahadi, 13 ga watan Mayu a filin da bada sadaka.

Wani marubucin shafin Tuwita mai suna Mustapha yace: “Wani dattijo a unguwanmu ya sayi fili jiya kuma ya bada kyauta ga makabarta saboda makabartan ya cika. Ya rasu da daddare kuma an birneshi a filin da safen nan.”

Wani abu babban darasi ne ga al’umman Musulmi masu hannu da shuni da su taimakawa addinin Allah kafin rayuwarsu ta zo karshe musamman yayinda azumin watan Ramadana ya gabato.

Allah ya sa mu cika da kyau da imani.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng