Yan bindiga sun kaiwa jirgin sojojin sama mai saukar angulu hari, sun kashe matukin jirgin
- Hukumar sojojin sama (NAF) ta bayyana cewa an kai hari a wurin saukar jirginsu mai saukar angulu, a Yenagoa, a ranar Lahadi
- NAF tace jami’ansu masu kula wurin sun kokarta wurin kare martabar wurin, inda sukaita harbe harbe tsakaninsu da ‘yan ta’addan
- Daraktan NAF mai kula da harkokin jama’a, Olatokunbo Adesanya, yace a ranar Lahadi, ‘yan ta’adda sun kai hari a wurin saukar jirginsu mai saukar angulu a Igbodene
Hukumar sojojin sama (NAF) ta bayyana cewa an kai hari a wurin saukar jirginsu mai saukar angulu, a Yenagoa, a ranar Lahadi.
NAF tace jami’ansu masu kula wurin sun kokarta wurin kare martabar wurin, inda sukaita harbe harbe tsakaninsu da ‘yan ta’addan.
Daraktan NAF mai kula da harkokin jama’a, Olatokunbo Adesanya, yace “a safiyar Lahadi, 13 ga watan Mayu 2018, ‘yan ta’addan wadanda ba’a san ko suwanene ba sun kai hari a wurin saukar jirginsu mai saukar angulu a Igbodene a Yanagoa, dake jihar Bayelsa.
“Duk da cewa jami’an tsaro dake aiki a lokacin sunyi kokri wurin tsayar da ‘yan ta’addan daga shiga wurin, wanda a kokarin hakan ne daya daga cikin matukan jirgin ya rasa rasansa.
KU KARANTA KUMA: Yadda jihohi 36 suka kasa N593.1bn daga watan Janairu zuwa watan Maris
“Shugaban hukumar Air Marshal Sadiq Abubakar, ya gaggauta byar da umurnin binciken abunda ya faru akan lamarin”, Mista Adesanya, air-vice-marshal ya bayyana haka.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng