Kannywood: An ba manyan jarumai lambar yabo (hotuna)
Masana’antar shira fina-finan Hausa ta Kannywood ta gudanar da gagarumin taro na fidda gwanaye.
An gudanar da taron ne domin ba manyan jarumai lambar yabo, sannan kuma an gudanar da na wannan shekarar ne a jihar Katsina a ranar Asabar, 12 ga watan Mayu.
Jarumin jarumai kuma babban darakta sarki mai Kannywood, wato Ali Nuhu ne ya lashe lambar yabo na gwarzon mai bada Umarni.
Haka zalika matashin jarumi wanda tauraronsa ke kan haskawa kuma fittacen mawaki Umar M. Sharif ya lashe lambar yabo na gwarzon jarumi mai tasowa.
KU KARANTA KUMA: Kannywood: Abubuwan da baku sani ba game da Maryam Babban Yaro
Daga karshe shahararriyar jaruma Halima Atete ta lashe lambar yabo na Gwarzuwar Jaruma.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng