Ana bikin Duniya: Bayan Mutuwar wani Sanata, yanzu haka ‘yan takara 21 ke zawarcin kujerarsa

Ana bikin Duniya: Bayan Mutuwar wani Sanata, yanzu haka ‘yan takara 21 ke zawarcin kujerarsa

Wutar siyasa na kara ruruwa a jahohin da za'a gudanar da zaben cike gurbi ciki har da Katsina wadda a yanzu haka tun kafin buga gangar siyasa ake ta bidirin neman kujerar Sanatan da ya rasu watan da ya gabata

Tun bayan Mutuwar Mustapha Bukar Sanata mai wakiltar Katsina ta Arewa a watan da ya gabata, tukunyar siyasar jihar ta rika zabalbala, zawarawan da suke burin maye gurbin gujerar marigayin suke ta kai kawo.

Ana bikin Duniya: Bayan Mutuwar wani Sanata, yanzu haka ‘yan takara 21 ke zawarcin kujerarsa
Ana bikin Duniya: Bayan Mutuwar wani Sanata, yanzu haka ‘yan takara 21 ke zawarcin kujerarsa

Ya zuwa yanzu haka dai masoya waccan kujera ta tsohon Sanatan sun kai kimanin Mutane 21 ne suka bayyana sha’awarsu ta maye gurbinsa a zauren Majalisar Dattijan a inuwar jam’iyyar APC.

Rahotanni dai sun bayyana cewa tuni dai garin na Katsina ya dauki harami duk kuwa da cewa Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ba ta bayyana lokacin da za’a gudanar da zaben cike gurbin ba, amma fastoci da hotunan ‘yan takarar na cigaba da zagawa a kafar sadarwa.

Wata majiya ta bayyana cewa, tsohon kakin majalisar jihar Katsina Umar Ya’u Gwajo Gwajo na daga cikin zawarawan kujerar, dama tare suka kara da Marigayin yayin da yake PDP a da.

Haka zalika suma ‘yan Majalisar tarayya da suka fito daga shiyyar Ahmed Babba Kaita (Mai wakiltar Kankia, Kusada, da Ingawa) da kuma Nasir Zangon Daura (Mai wakiltar Baure da Zango) suna daga cikin wadanda suka nuna sha’awarsu ta maye gurbin Marigayin.

KU KARANTA: To fa: Zai wahala Buhari ya kai bantansa a 2019 Inji Bafarawa

Shima kwamishinan Shari’a na jihar Ahmed El- Marzuq ya bi layi, da dan gidan tsohon wani Sanatan yankin da yake fada aji Mustapha Mahmud Kanti, sa Mai bawa gwamna shawara kan kimiyya da fasaha Dr. Rabe Nasir, da Mai bawa gwamanan Katsinan shawara kan harkokin zuba jari Ibrahim Zakari Talba suna daga cikin wadanda aka yi walkiya muka gansu.

Shahararren dan kasuwa Dr. Salisu Ahmad Ingawa, da Arch A.K. Ahmed,

Wanda ya tsaya takarar gwamna a zaben cikin gida na APC suma sun bi layin zawarcin kujerar.

Ragowar sun hada da Hon. Musa Haro, da Alhaji Abdullahi Bukar, da AIG Sani Ahmed (Mai ritaya), Tsohon dan majalisar wakilai Prof. Umar Adam Katsayal, da kuma Hon Lawal Garba.

Sai har ya zuwa yanzu, Mutane biyu ne kacal a jam’iyyar PDP suka bayyana ra’ayinsu na tsayawa takarar Sanatan, sune; Mani Nasarawa tsohon dan Majalisar wakilai da kuma Kabir Babba Kaita, wani jigo a PDP.

Ana bikin Duniya: Bayan Mutuwar wani Sanata, yanzu haka ‘yan takara 21 ke zawarcin kujerarsa
Ana bikin Duniya: Bayan Mutuwar wani Sanata, yanzu haka ‘yan takara 21 ke zawarcin kujerarsa

Masana dai na ganin cewa, za’a gwabza yaki babba wajen zaben cikin gida na jam’iyyar ta APC kasancewar mabukata sunyi yawa, amma inda suki zai samu shi ne idan wasu sun yarda su janyewa wasu.

Ana ta bangaren kuwa, hukumar zabe ta kasa ta ce har yanzu tana jiran umarni ne daga shugaban Majalisar Dattijan ta kasa don ya ayyana kujerar a matsayin gurbin da yake bukatar cikewa, kana ta shiga tsare-tsaren yadda za’a gudanar da zaben cike gurbin. A cewar Sakataren yada labarai na hukumar Mr Rotimi Oyekanmi.

A ranar 17 ga watan Afrilu ne shugaban hukumar zabe dai ta kasa Farfesa Mahmood Yakubu ya ce, akwai zabukan cike gurbi har guda hudu da hukumar zata gudanar; Mazabar Takum dake jihar Taraba, da Lokoja/Koton-Karfe dake jihar Kogi, da Bauchi ta Kudu Senatorial a jihar Bauchi, da kuma Katsina ta Arewa a jihar Katsina.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng