Siyasar Kaduna: Gobe asabar za'a kara tsakanin 'Masu mayen mulki' da 'tsinannu'

Siyasar Kaduna: Gobe asabar za'a kara tsakanin 'Masu mayen mulki' da 'tsinannu'

- Sanatocin Kaduna sun sha alwashin ganin bayan Gwamna a siyasance

- Shi kuma ya saka su gaba da rusau da tsinau

- Gobe take ranar hisabi

Siyasar Kaduna: Gobe asabar za'a kara tsakanin 'Masu mayen mulki' da 'tsinannu'
Siyasar Kaduna: Gobe asabar za'a kara tsakanin 'Masu mayen mulki' da 'tsinannu'

Ana sa rai, a Kaduna gobe, za'a yi zabukan kananan hukumomi lafiya a gama lafiya, duk da tsoron barkewar rikici tsakanin bangarorin jam'iyyar APC mai-mulki, wadda ta ware wasu a cikin gida take adawa dasu a cikin gida.

Gwamna Nasir Elrufai dai, yayi tofin Alla-Tsine ga Sanatocin jiharsa da suka hana jihar samun wani gwaggwafan lamuni daga bankin duniya, inda ya karanto wata kasidar bakantawa Sanatocin nasa rai a mako jiya.

Zabukan dai, ba lallai suyi wani armashi ba, ganin mai-jia shi kan kankane zabuka ko dori a sauran jihohi, duk da alkawarin gwamnan na yin adalci.

DUBA WANNAN: 'Yansanda sunyi babban kamu

Muddin dai wata jam'iyya ta kwashi garabasa, to kuwa za'a ga wasu manyan APC sun sauya sheka daga APC zuwa wannan jam'iyya, musamman ta PDP wadda tsohon gwamna Makarfi ke kokarin farfado da ita.

Babban zabe yana tafe a badi, kuma ana sa rai bayan zabukan firamare a cikin gida, da yawa zasu balla jam'iyyar su fice da jama'arsu, su fada wata jam'iyyar domin kawar da Tazarcen mai-rusai da tsinau.

Shi dai gwamna, ya koyi siyasar jiha ta qaranta da rawar gangi, inda har kira yayi da a aske wa dattijan jiharsa gemu in suka zo gida, kamar ba shine dan boko na lokacin mulkin Obasanjo ba. Watakil giyar mulki ce.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng