Ku raya tarihin da maifinku ya bari - Shugaba Buhari ya shawarci iyalan marigayi Isyaka Rabi’u
- Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci iyalana gidan Sheikh Isyaka Rabi’u, babban malami kuma babban dan kasuwa dasu raya tarihin da mahaifinsuya bari a doron kasa
- Shugaba Buhari wanda Boss Mustapha ya wakilta, Sakataren gwamnatin tarayya wurin janazar marigayi Sheikh Isyaka rabi’u a ranar Juma’a
- Shugaban kasar ya bukaci iyalan nasa dasu dage idan ma zasu iya su aje tarihi wanda yafi irin na mahaifin nasu kada su bari tarihin da mahaifin nasu ya kafa ya gushe
Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci iyalana gidan Sheikh Isyaka Rabi’u, babban malami kuma babban dan kasuwa da su raya tarihin da mahaifinsuya bari a doron kasa, kamarsu natsuwa da abotar kirki.
Shugaba Buhari wanda Boss Mustapha ya wakilta, Sakataren gwamnatin tarayya wurin janazar marigayi Sheikh Isyaka rabi’u a ranar Juma’a, a garin Kano.
Shugaban kasar ya bukaci iyalan nasa dasu dage idan ma zasu iya su aje tarihi wanda yafi irin na mahaifin nasu kada su bari tarihin da mahaifin nasu ya kafa ya gushe.
Cikin wadanda suka halarci janazar daga bangaren gwamnatin tarayya sun hada da Manjo-Janar Babagana Munguno (Rtd) mai bayar da shawara ta fannin tsaro na tarayya, Ministan harkokin ruwa Engr. Sulaiman Adamu, Ministan jiha na harkokin jiragen sama da kuma unguwanni, sannan sai Sanata hadi Sirika da Usman Jibril.
KU KARANTA KUMA: Buhari yayi ta’aziyya ga kungiyar CAN kan mutuwar sakataren ta
Daya daga cikin yaran marigayin kuma Ciyaman na BUA Group of companies, Abdulsalam Isayaka Rabi’u yayi godiya ga shugaban kasa da wannan muhimmiyar shawara da ya basu ta hanyar turo da wakilai na musamman da kuma kiran waya da yayi da kansa domin yi musu ta’aziya.
A yau Juma'a, 11 ga watan Mayu ne akayi jana'izar marigayin a jihar Kano.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng