Hukumar jarabawar shiga jami’a JAMB ta samu N8.5bn daga form na shiga manyan makarantu a shekarar 2018

Hukumar jarabawar shiga jami’a JAMB ta samu N8.5bn daga form na shiga manyan makarantu a shekarar 2018

- Hukumar jarabawa ta samu N8.5bn daga kudaden data siyar da form na shiga makarantun gaba da sakandare a najeriya na shekarar 2018

- Daya daga cikin manyan jami’an hukumar ne ya bayyana cewa an samu kudaden ne daga kudaden da dalibai 1,602,762 suka biya don neman shiga manyan makarantu

- Wasu kuma cikin kudin an samesu ne daga bangaren dalibai masu son shiga jami’a daga mataki na biyu wato DE

Hukumar jarabawa ta samu N8.453bn daga kudaden data siyar da form na shiga makarantun gaba da sakandare a najeriya na shekarar 2018, daga jaridar Premium Times.

Daya daga cikin manyan jami’an hukumar ne ya bayyana a safiyar Juma’a, cewa an samu kudaden ne daga kudaden da dalibai 1,602,762 suka biya, don neman shiga manyan makarantu dake fadin kasar a watan Mayu.

Wasu kuma cikin kudin an samesu ne daga bangaren dalibai masu son shiga jami’a daga mataki na biyu wato DE su 135,670, wanda kowane a cikinsu ya biya N5,000. Jami’in ya bukaci a boye sunansa saboda bai samu izinin hukumar ba kafin ya bayar da wannan jawabi game da hukumar.

KU KARANTA KUMA: Hawaye sun kwaranya yayinda aka binne Marigayi Isyaka Rabiu a Kano (hotuna)

Duk da cewa babu masaniyar ko nawa hukumar zata bawa gwamnatin tarayya bayan ta sallami masu wuraren da aka gudanar da jarabawowin da sauran abubuwa da kuma ma’aikatan hukumar masu kula da jarabawar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng