Dalilin da ya sa har yanzu nike cigaba da sa jar hula - Gwamna Ganduje

Dalilin da ya sa har yanzu nike cigaba da sa jar hula - Gwamna Ganduje

Gwamnan jihar Kano mai ci a yanzu Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa fatan da yake da shi na cewa a ko wane lokaci zai iya sulhuntawa shi da uban gidan sa kuma tsohon Gwamna jihar ta kano Dakta Rabi'u Kwankwaso ne ya sa ya ci gaba da yin anfani da jar hula.

Kamar dai yadda muka samu, a siyasar Kano da ma wasu bangarori a Najeriya, sanya jar hula na zaman wata alama da ke nuni da cewa mutum na goyon baya tare biyayya ga mazhabar darikar Kwankwasiyya.

Dalilin da ya sa har yanzu nike cigaba da sa jar hula - Gwamna Ganduje
Dalilin da ya sa har yanzu nike cigaba da sa jar hula - Gwamna Ganduje

Legit.ng ta samu haka zalika cewa ya zuwa yanzu kusan dukkan magoyan bayan Gwamna Gandujen tuni suka bar yin anfani da jar hular biyo bayan da rikicin da ya barke a tsakanin fitattun 'yan siyasar biyu da suka shafe tsawon lokaci suna tafiyar siyasa tare.

Gwamna Ganduje dai a baya cikin wata fita da yayi da majiyar ta BBC ya ce tuni jar hular ta sa ta dan yi fari-fari, kuma jan na daf da dusashewa kwata-kwata.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng