Kotu a Najeriya ta kulle wani babban malamin addini bisa zargin kashe masoyiyar sa

Kotu a Najeriya ta kulle wani babban malamin addini bisa zargin kashe masoyiyar sa

Wata kotun majistare dake zaman ta a garin Ifo dake a jihar Ogun a ranar Alhamis din da ta gabata ta bayar da umurnin cigaba da tsare wani babban malamin addinin kirista kuma shugaban majami'un Holy Garden Ministry mai suna Tobiloba Ipense.

Kamar dai yadda muka samu, kotun dai tana sauraron karar da aka shigar mata inda ake zargin babban malamin da kashe wata masoyiyar sa mai suna Raliat Sanni tare da binne ta a wani boyayyen wuri.

Kotu a Najeriya ta kulle wani babban malamin addini bisa zargin kashe masoyiyar sa
Kotu a Najeriya ta kulle wani babban malamin addini bisa zargin kashe masoyiyar sa

Legit.ng dai ta samu cewa tun farko jami'an 'yan sanda a unguwar Ewekoro ne suka kama babban malamin a ranar 26 ga watan Maris din da ya gabata.

A wani labarin kuma, Rundunar 'yan sandan jihar Bauchi dake a shiyyar Arewa ta gabas sun sanar da samun nasarar cafke akalla mutane 12 da suke zargi da hannu cikin kashe-kashen ban mamaki da ake yi a jihar.

Kamar dai yadda jami'in hulda da jama'a na rundunar mai suna DSP Kamal Datti Abubakar ya shaidawa manema labarai, garin na Bauchi a wasu unguwannin da suka hada da Fadaman Mada da Gida Dubu suna fama ne da kisan mutane a wani yanani mai ban mamaki.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel