Kowa da kiwon da ta karbe shi: Yaron Ministan Buhari ya tsunduma harkar waka

Kowa da kiwon da ta karbe shi: Yaron Ministan Buhari ya tsunduma harkar waka

- Yaron ministan Buhari ya koma harkar wakewake

- Kach ya yi wakar tare da Sanata Dino Melaye

Tabbas, bahaushe ya yi gaskiya, kowa da kiwon da ta karbe shi, anan ma wani matashine mai suna Uche Kachikwu, wanda mahaifinsa ne karamin ministan man fetir ya rungumi harkar wakokin zamani, inda ya fada kamfanin wakoki na MMMG.

Jaridar The Cables ta ruwaito shugaban kamfanin mai suna Ubi Franklin ne ya sanar da shigar Uche, wanda aka fi sani da suna Kach a shafinsa na Instagram a ranar Alhamis, 10 ga watan Mayu.

KU KARANTA: Yan bindiga sun hallaka mutane 3 yayin da suka kai wani mummunan hari a Masallaci

Kowa da kiwon da ta karbe shi: Yaron Ministan Buhari ya tsunduma harkar waka
Kach da Ubi

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Kach na daga cikin yayan karamin ministan albarkatun ministan man fetir, kuma tsohon shugaban hukumar tace albarkatun man fetir, Ibe Kachikwu.

Sai dai wani abu mai daukan hankali a cikin wakar da Kach yayi mai suna ‘Dino’, shi ne fitowar Sanatan nan da ya yi kaurin suna, Sanata Dino Melayye

Kowa da kiwon da ta karbe shi: Yaron Ministan Buhari ya tsunduma harkar waka
Dino da Kach

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel