An ba wa kamfanoni 13 lasisin kafa kananan matatun man fetur

An ba wa kamfanoni 13 lasisin kafa kananan matatun man fetur

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ba wa wasu kamfanoni akalla 13 lasisin samun damar gina kananun matatun mai a yankin Neja Delta mai arzikin man fetur dake kudu maso kudancin Najeriya.

Mun samu cewa kimanin kamfanoni 35 ne dai suka nemi lasisin sai dai amma 13 ne kadai suka samu lasisin na gina matatun bayan kammala sharuddan da aka gindaya masu.

An ba wa kamfanoni 13 lasisin kafa kananan matatun man fetur
An ba wa kamfanoni 13 lasisin kafa kananan matatun man fetur

Legit.ng ta samu cewa da yake karin bayani, shugaban hukumar rukunin kamfanonin NNPC na Kasa, Mista Maikanti Baru ya bayyana cewa hukumar ta bi dukkan dokoki wajen bayar da lasisin.

A wani labarin kuma, Sanatoci uku dake wakiltar jihar Kaduna a majalisar dattijai sun rubuta wata doguwar takardar korafi suna mai kai karar gwamnan jihar su Malam Nasir El-rufai zuwa ga shugaban kasar Najeriya Shugaba Muhammadu Buhari.

Sanatocin da suka hada da Sanata Shehu Sani, Sanata Suleiman Hunkuyi da kuma Sanata Danjuma Laah sun kai karar gwamnan ne ga shugaban kasa bisa ga kalaman da suka kira na nuna asalin kiyayya da Gwamnan ya yi a wajen taron siyasa a satin da ya gaba.

dan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel