Kalaman kin jini: Sanatocin jihar Kaduna sun kai karar Gwamna El-Rufai ga Buhari
Sanatoci uku dake wakiltar jihar Kaduna a majalisar dattijai sun rubuta wata doguwar takardar korafi suna mai kai karar gwamnan jihar su Malam Nasir El-rufai zuwa ga shugaban kasar Najeriya Shugaba Muhammadu Buhari.
Sanatocin da suka hada da Sanata Shehu Sani, Sanata Suleiman Hunkuyi da kuma Sanata Danjuma Laah sun kai karar gwamnan ne ga shugaban kasa bisa ga kalaman da suka kira na nuna asalin kiyayya da Gwamnan ya yi a wajen taron siyasa a satin da ya gaba.
Legit.ng dai ta samu cewa sun bukaci shugaban kasar da ya shiga tsakanin su tare kuma da basu kariya domin rayuwar su na cikin hadari.
A wani labarin kuma, Babbar jam'iyyar adawa ta PDP kamar yadda muka samu kawo yanzu haka dai ta kammala shirin ta na yi kutungwilar tsayar da tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Alhaji Atiku Abubakar a matsayin dan takarar ta da zai kara da shugaba Muhammadu Buhari a 2019.
Wannan dai kamar yadda muka samu, majiyar mu ta Vanguard ta ce ta samu tabbacin hakan ne daga wajen wani jigo a jam'iyyar wanda kuma ya bukaci a sakaya sunan sa a ranar Larabar da ta gabata.
dan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng