2019: Kungiyar Dattawan Arewa za ta yi taron makomar siyasar yankin

2019: Kungiyar Dattawan Arewa za ta yi taron makomar siyasar yankin

Shugaban Kungiyar Dattawan Arewa, Tanko Yakasai, ya sanar da cewa nan ba da jimawa ba kungiyar su za ta gudanar da gagarimin taro akan makomar siyasar yankin.

Yakasai ya kara da cewa taron, zai kunshi ‘yan siyasar yankin Arewa ne daga bangarori daban-daban.

Ya yi wannan bayani ne jiya Laraba 9 ga watan Mayu a lokacin da kungiyar ta su ta kai ziyara ga Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki.

Yakasai ya ce taron gangamin zai yi magana ne a kan wasu kalubale da aka san sun dami Arewacin kasar.

Daga nan sai ya roki Majalisar Dattawa da ta goyi bayan taron tare da goyon bayan gudanar da shi.

Yakasai ya fada wa Saraki cewa sun akai masa ziyarar ce domin su sanar da shi dalilin kafa kungiyar, manufofin ta da kuma muradin da ta ke son ta cimma.

2019: Kungiyar Dattawan Arewa za ta yi taron makomar siyasar yankin
2019: Kungiyar Dattawan Arewa za ta yi taron makomar siyasar yankin

Ya ce ba gaskiya ba ne da ake ta yada ji-ta-ji-tar cewa sun je ne domin neman su fito da dan takarar zaben shugaban kasa daya tal. Ya ce su dai su na neman gudummawar hadin kai daga ‘yan Najeriya, masu hangen nesa da kyawawan manufofi.

Saraki ya yaba da kungiyar, kuma ya nuna cewa lokaci ya yi da za a hada kai a samar dauwamammnen zaman lafiya a kasar nan.

KU KARANTA KUMA: Kotu ta ajiye hukuncin bayar da Dino Melaye beli zuwa ranar 16 ga watan Mayu

Ya ce a matsayin su na shugabanni kuma ‘yan siyasa, akwai nauyi kan su wajen samo hanyoyin da za a warware matsalolin da ke kawo wa kasar nan tarnakin ci gaba.

Ya cigaba da cewa babu shakka akwai matsaloli, kuma dama an ce barin abinci a ciki ba a maganin yunwa.

Wadanda suka halarci taron sun hada da Alhaji Tanko Yakasai, Ibrahim Mantu, Dr. Bello Halilu, tsohon gwamnan Niger Mu’azu Babangida Aliyu da kuma tsohon gwamnan jihar Kogi Idris Wada, sun gudanar da taron a wani bangare na majalisa.

Sauran wadanda suka halarci taron sune tsohon ministan birnin tarayya Bala Mohammed da Abba Gana, tsohon ministan al’amuran mata Hajiya Inna Ciroma, Dr. Umar Ardo, Hajia Zainab Maina, Dr. Mamman Shata, da kuma Sanata Joseph Waku.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel