Ko ba mutuwa akwai tsufa: Wani tsoho mai shekaru 104 ya kai kansa ga halaka alhalin yana sane

Ko ba mutuwa akwai tsufa: Wani tsoho mai shekaru 104 ya kai kansa ga halaka alhalin yana sane

Wani tsohon farfesan ilimin kimiyya, Dakta David Goodall mai shekaru 104 ya dauki matakin kawo karshen rayuwarsa ta hanyar kashe kansa da taimakon wasu kwararun likitoci dake aiki a wani asibitin dake da lasisin kashe mutane idan har sun amince, inji rahoton jaridar Punch.

Wannan tsoho ya bayyana ma Duniya a ranar Laraba, 9 ga watan Mayu cewa shi kam ya gaji da rayuwar Duniya, duk da cewa ba shi da wata cuta, amma fa baya jin dadin rayuwa a yadda take, don haka ya nemi taimakon yadda zai kashe kansa, amma kasarsa ta Austreliya ta hana shi damar.

KU KARANTA: Wannan abin kunya har ina: An kama Uba da Dansa sun saci naira miliyan 2.4

Sai dai abinka da tsoho, sai ya nemi taimakon wata cibiyar kashe kai dake kasar Switzerland, inda suka amince masa, don haka ya garzaya kasar tare da iyalansa da nufin kawo karshen rayuwarsa a ranar Alhamis, 10 ga watan Mayu.

Ko ba mutuwa akwai tsufa: Wani tsoho mai shekaru 104 ya kai kansa ga halaka alhalin yana sane
Goodall yayin bayyana dalilin kashe kansa

Majiyar Legit.ng ta ruwaito da yake ganawa da manema labaru a ranar Laraba, jajibarin mutuwarsa, Goodall yace: “Na yi mamakin yadda mutane ke ta cecekuce game da ni a shafukan yanar gizo, na gode da karamcin da kasar Australia ta bani, tare da damar da suka bani na zuwa nan don kashe kaina.

“Abinda duk mutumin da ya kai shekaruna ke bukata shi ne ya samu damar kawo karshen rayuwarsa ta yadda ya so a lokacin da ya so. Karfin sarrafa gabban jikina ya ragu sosai, kuma yana cigaba da raguwa, bana son cigaba da rayuwa, na ji dadi da na samu damar mutuwa a gobe, kuma na yaba da kokarin likitocin cibiyar nan.” Inji Goodall.

Daga karshe Goodall ya gode ma iyalansa da suka fahimce shi, sai dai yace zai bukaci a sanya wata wakar ‘Beethoven ninth symphony’ a lokacin da zai mutu, bayan nan yan jaridu da yan uwansa dake wajen suka yi masa tafi a lokacin da ya kammala jawabinsa.

A ranar Alhamis 10 ga watan Mayu ne za’a kashe Goodall kamar yadda ya bukata a gaban Iyalai, yan uwa da abokan arzikinsa da suka rako shi daga Australia zuwa kasar Switzerland.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng