Marashi ya shiga uku: Ƴaƴan Mai Gida sun lakaɗawa Miji da Mata dukan tsiya kan kuɗin haya

Marashi ya shiga uku: Ƴaƴan Mai Gida sun lakaɗawa Miji da Mata dukan tsiya kan kuɗin haya

- Maras shi baya zuciya in ji masu iya magana, amma a yau har kotu wasu yan haya suka kai 'ya'yan mai gidan da suke haya bisa dukan su da su kayi

- Bayan karanto musu laifinsu 'ya'yan mai gidan sun ce su ba su san zancen ba

An gurfanar da Isiaka Olaleye and Olaide Olaleye a gaban kuliya bisa laifin lakaɗawa ƴan hayan gidansu Miji da Matarsa na jaki kan rashin biya kuɗin haya.

Marashi ya shig uku: Ƴaƴan Mai Gida sun lakaɗawa Miji da Mata dukan tsiya kan kuɗin haya
Marashi ya shig uku: Ƴaƴan Mai Gida sun lakaɗawa Miji da Mata dukan tsiya kan kuɗin haya

Faruwar lamarin ke da wuya sai suka kai kara ofishin 'yan sanda, inda nan take a kame su wasu kuma suka arce.

Waɗanda ake zargin dai sun yi lugude ne kan Mijin mai suna Isiaka da Matarsa wadda take sana'ar ɗinki, an gurfanar da su ne gaban mai shari'a Mrs F.F. George bisa zargin aikata laifuka uku; tayar da hankali da tuggu tare da dukan masu ƙarar.

Marashi ya shig uku: Ƴaƴan Mai Gida sun lakaɗawa Miji da Mata dukan tsiya kan kuɗin haya
Marashi ya shig uku: Ƴaƴan Mai Gida sun lakaɗawa Miji da Mata dukan tsiya kan kuɗin haya
Asali: UGC

Ɗan sanda mai gabatar da ƙara Godwin Awase ya bayyanawa kotun cewa waɗanda ake zargin sun aikata laifin ne ranar 6 gawatan Mayu a unguwar Onipanu ta jihar Legas.

KU KARANTA: Mutane 3 masu tsananin taurin kai da kunnan kashi a Gwamnatin Buhari

Sannan ya cigaba da cewa, 'ya'yan mai gidan sun yi hadin baki ne da wasu 'yan daba wajen yiwa 'yan hayan gidan Mr Sheu Adeniran da matarsa dukan tsiya tare kuma da shiga dakin su ba bisa izini ba sannan suka rika wurgi da kayayyakinsu waje.

Bayan sun ki amicewa da aikata laifin ne alkali ya bayar da su beli kan kudi Naira N50,000 kowannensu da kuma wadanda zasu tsaya musu da suke da takardar shaidar biyan haraji ga gwamnatin jihar Legas ta tsawon shekaru biyu.

Wannan dai laifi ne da ya sabawa sashi na 168,171 da kuma 411 na kundin manyan laifuka na jihar Legas 2015. Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel