Mutane 3 masu tsananin taurin kai da kunnan kashi a Gwamnatin Buhari
- Jadawalin sunayen Mutane masu tsattsauran ra'ayi da kuma kunnan kashi tare da irin kwamacala da kuma cakwakiyar da suka shiga a cikin tsawon loakcin da suke rike da mukamai a Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari
Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta ba shekaru uku baya kuma abubuwa da yawa sun farun na ƙoƙari da kuma jajircewa da Gwamnatin tayi kan abubuwa da dama da kuma waɗanda suka bayar da mamaki ga ƴan Najeriya.
Daga ciki abubuwan ban mamakin da suka faru akwai batun nan na sace kasafin kuɗi a Majalisar ƙasa da sace sandar iko ta Majalisar da kuma labarin Ɓerayen nan da suka hana shugaban ƙasa zama a ofishinsa bayan dawowa daga jiyya daga birnin Landan.
Amma sai dai da batun taurin kai da rashin jin magana da wasu masu rike da manyan muƙamai a Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ke nunawa abun dubawa ne, a don haka ne Legit.ng ta shirya muku wannan gajeran rahoton.
KU KARANTA: Na shiga ban dauka ba: Wata mai aikin gida ta saci gwalagwalai na Miliyoyin Nairori
Legit.ng ta yi nazarin kan wasu masu riƙe da madafun iko huɗu da su kayi ƙaurin suna wajen yin gaban kansu ko kuma faɗin abinda suka ga dama kuma ba tare da fuskantar wani hukunci ba.
Farfesa Itse Sagay
Shi ne shugaban kwamitin da yake baiwa shugaban ƙasa shawara kan yaƙi da cin hanci da rashawa.
Yazo mana a na ɗaye ne duba da zurfin iliminsa da kuma shekarunsa.
Irin ɓaranɓaramar da yake yi kuma ba wani matakin da ake ɗauka a kansa na da yawan gaske, domin hatta Buharin ma bai kyale ba, don kuwa ya sha caccakarsa da bashi shawarwari da ba kasafai wanda aka naɗa mukami ke iya fadawa uban gidansa ba.
Ya kuma sha ya faɗawa ƴan majalisa maganganun da ya ga dama kuma ba mai iya yi masa komai, kamar ko a jiya 9 ga watan da muke ciki sai sai da ya caccaki 'Yan Majalisar Dattijai bisa cewa da sukai Babban Sufeton 'Yan sanda na ƙasa makiyin Dimukuraɗiyya ne.
Hameed Ali
Tsohon Soja baka san wasa ba sai dai aiki, shi ne irin kirarin da ake yi masa.
Shugaba. Muhammadu Buhari ya naɗa shi muƙamin Shugaban hukumar kwastam ta ƙasa amma sai da ya ja aji kafin ya amsa zai karɓi muƙamin, domin kuwa sai da ya shafe tsawon satittuka kafin ya karɓi muƙamin.
Bayan kuma ya karɓa sai yaƙi sanya kayan sarkin da suke sanyawa a hukumance, wanda hakan yayi sandiyyar sanya kafar wando ɗaya da shi da Majisar Dattijai ta ƙasa. Lamarin da yayi tsananin ɗaukar hankalin kafafen yaɗa labarai da ma ƴan Najeriya baki ɗaya.
Majalisar dai ta sha gayyatarsa don yazo da kakin aikin kwastam amma yaƙi sanyawa har ya zuwa yau da muke haɗa wannan rahoto.
Rigimar baya-bayan nan da ta faru tsakaninsa da Shugabannin kwamitin kula da kashe-kashen kuɗaɗe a hukumar kwastam Dino Melaye abin bayar da misali ce.
Amma kuma hukumar ta tara kudade masu tarin yawa a karkashin shugabancinsa.
IGP Ibrahim Idris
Daga fari kamar baya cikin lissafin masu kunnen ƙashi duba kasancewarsa jami'in tsaro mai muƙamin ƙololuwa a hukumar 'Ya sanda, har sai da ya bijirewa umarnin shugaban ƙasa kan cewa ya tattara nasa ya nasa ya koma jihar Benue don zai fi mayar da hankali wajen magance matsalar tsaro da taƙi ci taƙi cinyewa a jihar.
Rashin hukuncin da ba'a ɗauka akansa ba ya sanya ba'a yi mamakin irin fatalin da yake yi da gayyatar da Majalisar Dattijai ta yi masa har sau 3 shi kuma yana kin zuwa ba.
Rashin zuwan nasa ya sanya Majalisar ta ayyana shi a matsayin makiyin Dimukuraɗiyya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng