Boko Haram: An kashe Maciji ba’a sare kansa ba – Inji Majalisar dinkin Duniya

Boko Haram: An kashe Maciji ba’a sare kansa ba – Inji Majalisar dinkin Duniya

Wakilin babban sakataren Majalisar dinkin Duniya, Anthonio Gutteres, Dakta Muhammad Ibn Chambers ya bayyana kungiyar ta’addanci ta Boko Haram a matsayin macijin da ake kashe, amma ba’a sare kansa ba, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Chambers yana cewa zuwa yanzu kokarin da gwamnatin kasar Najeriya ke yi wajen amfani da Dakarun Soji wajen yaki da yan ta’addar ya karya lagon yan ta’addan, amma fa har yanzu ba’a gama yakin ba.

KU KARANTA: Jana’izar Sheikh Isiyaka Rabiu: Gwamnatin jihar Kano ta sanar da ranar hutu

Chambers ya bayyana hake ne a ranar Laraba 9 ga watan Mayu, a yayin taron gwamnonin yankin tafkin Chadi da ya gudana a garin Maiduguri na jihar Borno da aka yi shi don lalubo hanyoyin tabbatar da zaman lafiya dawwamamme a yankin.

Boko Haram: An kashe Maciji ba’a sare kansa ba – Inji Malisar dinkin Duniya
Boko Haram

“Gaskiya ba a gama da Boko Haram ba har yanzu, amma tabbas an gurguntasu, don haka ya zama wajibi a cigaba da yakin.” Inji Dakta Muhammad Ibn Chambers.

Daga karshe Chambers yace majalisar dinkin Duniya da sauran kasashen Duniya za su cigaba da baiwa Najeriya goyon baya da gudunmuwar da suka dace don ganin an kakkabe ayyukan ta’addanci na kungiyar Boko Haram daga yankin tafkin Chadi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng