Makiyin Dimukradiyya: Babban Sufetan Yansandan Najeriya ya mayar wa majalisar dattawa martani

Makiyin Dimukradiyya: Babban Sufetan Yansandan Najeriya ya mayar wa majalisar dattawa martani

Babban Sufetan Yansandan Najeriya, IG Ibrahim Idris ya bayyana gayyatar da yayan majalisar dattawa suka yi masa a matsayin wata dama da suke neman amfani da ita wajen tabbatar da sun kawo tasgaro ga tsarin shari’a, hukunci da tabbatar da gaskiyar mai gaskiya.

Premium Times ta ruwaito Sufetan wanda har sau uku majalisa na gayyatarsa yana cewa bai ga dalilin gurfana a gaban majalisar dattawan ba, don haka ne yayi shakulatin bangaro da umarnin majalisar.

KU KARANTA: Ana dakon manyan jirage guda 32 dauke da man fetir da kayayyakin abinci zuwa Najeriya

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a ranar Laraba 9 ga watan Mayu ne majalisar ta bayyana Sufetan a matsayin makiyin Dimukradiyya, wanda bai dace ya rike wani mukami ba, biyo bayan yin watsi da umarninta na cewa ya gurfana a gabanta, a karo na uku.

Makiyin Dimukradiyya: Babban Sufetan Yansandan Najeriya ya mayar wa majalisar dattawa martani
Majalisa

Manufar gayyatar da majalisar ta yi ma Sufetan ya ta’allaka ne ga matsalolin tsaro dake faruwa a kasar nan, a cewarsu, amma Sufetan yace ya gano cewa wata kitimurmura da cin fuska yayan majalisar suka shirya masa, musamman game da bahallatsar Sanata Dino Melaye, don haka yace bai yadda da idanuwansa biyu ba amma ya fada gadar zare.

Sufetan ta bakin Kaakakin rundunar Yansanda, Jimoh Moshood ya bayyana wasu sassan kundin tsarin mulkin kasar nan da suka bashi damar kin amsa gayyatar majalisar. “Duba da sashi na 215 (a) da kuma kundin dokokin rundunar Yansanda sashi na 309 (1) sun bayyana cewar manyan Yansanda zasu iya gudanar da ayyukan babban Sufetan, ko su wakilce shi idan har ya basu uamrni.”

Makiyin Dimukradiyya: Babban Sufetan Yansandan Najeriya ya mayar wa majalisar dattawa martani
Babban Sufetan Yansandan Najeriya

Kaakakin yace Sufetan ya aika da wasu manyan jami’an Yansanda dasu wakilce shi a wannan zama, amma suka yi ma wakilan nasa korar kare, wai su ala dole sai Sufetan ya bayyana a gabansu, ya kara da cewa sai da IG ya aika ma shugaban majalisar dattawa wasika cewa ba zai gurfana a gabansu ba, don kuwa ya fahimci sun shirya ci masa mutunci ne.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel