Yadda PDP ke son 'cin kasuwa' daga rashin lafiyar shugaba Buhari
- An ji rade-radin cewa shugaba Buhari ya fadi a kasar Amurka da rashin lafiya
- Shugaban bai bayyana me ke damunsa ba, kuma yana son takara
- Masu hasashe na gani rashin lafiyar na iya kashe wa masoyanshi gwiwa
Shin ya zata kasance muddin lafiyar shugaba Buhari ta gurgunta kafin a kai ga zaben shugaban kasa watanni 10 masu zuwa?
Wannan ita ce tambayar dake bakin kowa, musamman wadanda ke cikin APC jam'iyya mai mulki, wadanda gaba-dayansu a babbar rigar shugaban suke lilo.
A baya-bayan nan, an jiyo rade-radin karkashin kasa da ke cewa shugaba Buharin ya fadi da sabuwar rashin lafiya a yayin ziyararsa ta Amurka, wadda ta sanya dole aka garzaya dashi Ingila maimakon ya dawo Najeriya.
Duk da babu tabbas ga wannan batu, shugaban ya sake komawa ganin likita a makon nan domin ya ga likita, wanda hakan ya sanya PDP ta sake kambama batun don gurgunta siyasar masu mulkin.
DUBA WANNAN: Turawa sun sake kira a canja al-kur'ani
A zahiri dai, muddin shugaban yayi takara, to yana da kusan tabbas ta iya lashe zabe, musamman a yankunan arewa da yamma ta Najeriya, inda ake masa biyayyar makanta.
Amma kuma, muddin aka kula cewa lafiyar tasa bata iya bari yayi wani mulki mai kyau a karo na biyu, aka kuma kalli wa zai gaje shi, kuma a hannun suwa mulkin zai fada, kamar su Tinubu Ahmad na Legas, tagomashin cin zabensa ka iya bashi kashi a zabukan 2019.
Wannan yasa PDP ke son kambama rashin lafiyar shugaban, domin nata 'yan takarar, musamman irinsu Atiku Abubakar, da Sule Lamido, su iya samun wani katabus a babban zaben.
Shugaba Buhari dai bai bayyana gaba-daya me ke damunnsa ba, kuma rufa-rufar da mukarrabansa kanyi kan lafiyarsa na jawo rade-radi na babu gaira babu dalili.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng