Duk masu cewa kada Buhari ya tsaya takara tsoran shi suke ji- Jigo a APC

Duk masu cewa kada Buhari ya tsaya takara tsoran shi suke ji- Jigo a APC

- Gwuiwar yan jam'iyyar APC ya kara karfi game da takarar Muhammadu Buhari a 2019

- Wani jigo a jam'iyyar daga yammacin kasar nan ne ya ce, falan daya kawai Buharin zai lashe kuri'un yankin

Shugaban jam'iyyar APC reshen jihar Legas Chief Henry Ajomale yatabbatar da cewa duk masu kira da kada Muhammadu Buhari ya tsaya takara tsoronsa suke ji kawai. Ajomale ya bayyana hakan ne a wata hira da ƴan jaridua jihar ta Lagas.

Duk masu cewa kada Buhari ya tsaya takara tsoran shi suke ji- Jigo a APC
Chief Henry Ajomale

A cewarsa, Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yayi mutuƙar ƙoƙari wajen cika alƙawurran da ya ɗauka bayan da aka zaɓe shi a 2015. Kuma yasan Mutanen ƙasar nan na bayansa

Domin jam'iyyar PDP a zamanin gwamnatin da ta gabata sun yi ta cewa komai na kasar nan yana tafiya dai-dai a fannin tattalin arziƙi, sai da muka zo duk muka ga ba haka bane bayan kuma mun yi shirye-shiryenmu a kan tattalin arziƙin da suka ce lafiyar shi kalau.

Kuma duk wanda kaji yana cewa kada Buhari ya tsaya takara to baya zaɓe ne, irinsu ne masu ɗaukar ranar zaɓe tamkar ranar hutu a gare su.

KU KARANTA: Soyayya ta koma kiyayya: Uwargida yar shekara 16 ta kashe Mijinta da maganin ɓera a jihar Kano

Daya yake amsa tambaya kan cewa ko Buhari yayi wani abin kataɓus a yankin Kudu maso yammacin Najeriya da ya kamata a sake zaɓarsa, cewa yayi babu wani yanki da zai ce ya samu abinda ya ke so ɗari bisa ɗari ba, amma dai ya tabbata Shugaba Muhammadu Buhari zai lashe zaɓen yankin yarbawan baki ɗaya.

Tun bayan baiyana aniyarsa ta sake tsayawa takara, Shugaba Muhammadu Buhari yake cigaba da shan suka daga ɓangarori daban-daban.

Wasu na ganin bai tabuka wani abin azo a gani ba yayin da wasu kuma suke kallon bashi da cikakkiyar lafiyar cigaba da mulki a 2019.

Duk da irin wannan cecekuce da batun sake tsayawa takararsa ya haddasa gwamnonin APC sun bayyana aniyarsu ƙarara ta goyon sake fitowa takararsa a kakar zaɓe mai zuwa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel