Hanyoyi 4 da ake kawar da radadin cizon cinnaka cikin gaggawa

Hanyoyi 4 da ake kawar da radadin cizon cinnaka cikin gaggawa

Ina da tabbacin kowannen mu ya san radadin cizon cinnaka da yadda ya ke fitar da mutum a cikin hayyacin sa na wani lokaci, musamman ma idan cinnakan ya shiga riga ko wando ya sassarfa cizo a gurare da dama.

Toh sai dai duk da zafin wannan radadi, yawanci haka ake daurewa har lokacin da ya ga dama ya tafi da kan shi.

Akwai hanyoyi da dama masu sauki da za a iya magance radadin cizon cinnaka cikin gaggawa.

Hanyoyi 4 da ake kawar da radadin cizon cinnaka cikin gaggawa
Hanyoyi 4 da ake kawar da radadin cizon cinnaka cikin gaggawa

A gwada wadannan hanyoyi 4, za a ga fa'ida:

1. Za a matse lemon samin a shafa ruwan a gurin da cinnakan ya yi cizo ko kuma a yanka shi kawai a shafa a gurin. A cikin dan kankanin lokaci za a samu saukin radadin. Banda radadin ya na kuma magance kumburi.

2. Ita kuma yanka ta a ke yi, sai a dora ta akan gurin da cinnaka ya yi cizo a bar shi na wani lokaci. Kamar sauran, cikin kankanin lokaci za a samu saukin radadin.

3. A nemi zuma a shafa ta a inda cinnakan ya yi cizon. Ta na kunshe da sinadaran da ke taimakawa wajen rage radadin tare da kumburin da cizon ya haifar.

KU KARANTA KUMA: Hanyoyi 5 da mace zata mallaki miji cikin sauki

4. A samu a dora kankara a dora a kan gurin cizon, nan da nan za a ji saukin radadin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng