Kashin kadangare matasa ke zuka yanzu don maye – Likitan mahaukata, Taiwo Sheikh
Shugaban kungiyar likitocin mahaukata a Najeriya, Dakta Taiwo Sheik ya bayyana cewa sabon binciken da aka gudanar ya nuna cewa kasha 85 cikin 100 na mahaukata a Najeriya matasa ne masu shekaru tsakanin 18-38
Likitan ya bayyana wannan ne a wani hira da yayi da jaridar Daily Independent inda yace babban kalubalen haukacewa a Najeriya ya wuce amfani da kwayoyi yanzu, matasa na zukan kashin kadangare domin shiga maye.
Yace: “Matansanmu na shan kashin kadangare yanzu, sun cusa hanci cikin masai, suna shan garin ashana. Abinda ya wuce amfani da kwayoyin asibiti yanzu.”
KU KARANTA: Hukumar NAFDAC ta datse kamfanoni 3 a Kudancin Najeriya
Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa Hukumar kula da kafa dokoki akan kayan abinci da magunguna ta Najeriya watau NAFDAC, (National Agency for Food and Drug Administration & Control), ta datse wasu manyan kamfanoni uku na magunguna dake kudancin kasar nan ta Najeriya.
Hukumar ta NAFDAC ta datse kamfanin Peace Standard Pharmac*utical Limited, Bioraj Pharmac*utical Limited da kuma kamfanin Emzor Pharmac*uticals Ind. Ltd sakamakon sanya hannayen su cikin takaddamar maganin nan tari na Codeine.
Mun samu wannan rahoton ne da sanadin shugaba ta hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye, da ta bayyana cikin wata sanarwa a ranar Litinin din da ta gabata.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a: https://facebook.com/naijcomhausa https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng