Mutane 3 Uku sun mutu a wani tashin tashin da ya wakana a jihar Nassarawa

Mutane 3 Uku sun mutu a wani tashin tashin da ya wakana a jihar Nassarawa

Akalla mutane uku ne suka gamu da ajalinsu a wasu kauyukan Azara da Kadarko dake cikin karamar hukumar Keana na jihar Nassarawa, yayin da wasu yan bindiga makiyaya suka kona gidaje guda 13, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wasu manoman kabilar Tibi sun jikkata, baya da wadanda suka mutu, a harin na ranar Juma’a da ta gabata, inda makiyayan dauke da muggan makamai suka afka musu ba jinni ba gani.

KU KARANTA: Abin kunya: Yadda wani Uba da Dansa suka zakke ma wata Yarinya mai shekaru 9 a Katsina

Dayake tabbatar da faruwan harin, shugaban kungiyar matasan kabilar Tibi na jihar Nassarawa, Benjamin Ngitamen yace zaman tattaunawa da aka yi tsakanin Fulani makiyaya da yan kabilar Tibi manoma bai haifar da da mai ido ba.

Ngitamen ya bayyana haka ne cikin bacin rai, inda yace har yanzu kashe kashen da suke zargin Fulani makiyaya ne ke yinsu basu tsaya ba, musamman a lunguna da sauran kauyukan jihar, ya kara da cewa wani Bafulatani a kauyen Kadarko, inda ya sassareshi da adda, kuma suka kone gidaje uku.

“Muna kira ga gwamnatin jihar ta turo da Sojoji, Yansandan da sauran jami’an tsaro don tabbatar da zaman lafiya tare da kwantar da tarzoma, domin manoman Tibi su samu damar zuwa gonakinsu, haka zalika mutane da dama dake sansanonin yan gudun hijira na cikin damuwa.” Inji shi.

Shugaban matasan ya cigaba da fadin yan bindigan sun kona akalla gidaje 10 a karamar hukumar Awe na jihar, inda suka kashe wasu matasan Tibi da suka hada da Shagora Daniel da abokanansa, daga karshe yayi kira ga kungiyar Miyetti Allah ta hana yayanta aikata wadannan munanan ayyuka.

Sai dai a nasa jawabin, Kaakakin Yansandan jihar, DSP Kennedy Idrisu ya tabbatar da harin, amma ya musanta adadin mutanen da aka ruwaito sun mutu, inda yace mutum daya ne ya mutu a harin na ranar Juma’a, yayin da wasu suka samu rauni daban daban.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel