Karfin hali: ‘Yan Najeriya 17 da suka tsallake nitsewa cikin kogi sun kai kasar Italiya kara (Hotuna)

Karfin hali: ‘Yan Najeriya 17 da suka tsallake nitsewa cikin kogi sun kai kasar Italiya kara (Hotuna)

-

- Zuwa kasashen Turai da 'yan Nahiyar Africa suke yi cirani na cigaba da salwantar rayuwarsu

- aWasu yan cirani da suka gamu da matsala a yunkurinnsu na tsallakawa Turan sun bayyana yadda aka ci zarafinsu

Kungiyar bayar da agaji ta Global Action Network, ta bayyana cewa a ranar 6 ga watan Nuwamba 2017 ne, jami’an tsaron kan teku na kasar Libya suka dakile yunkurin ceto wasu kwale-kwale 3 da suke shirin shiga kasar Italiya. wanda hakan yayi sandiyyar mutuwar ashirin daga cikin Mutane 130.

Karfin hali: ‘Yan Najeriya 17 da suka tsallake nitsewa cikin kogi sun kai kasar Italiya kara (Hotuna)
Karfin hali: ‘Yan Najeriya 17 da suka tsallake nitsewa cikin kogi sun kai kasar Italiya kara (Hotuna)

'Yan ciranin dai an boye sunayensu, amma wata lauya mai suna Violeta Moreno-Lax, dake aiki da kungiyoyin fafutukar kwato hakkin dan Adam ta bayyana cewa, tabbas tana daga cikin lauyoyi hudun da zasu wakilci masu karar a jiya Talata.

KU KARANTA: Mafusatan samari sun farwa fitaccen dan siyasa don ya goyi bayan tazarcen Buhari

An dai rawaito cewa, yayin da kwale-kwalen nasu yake fuskantar nitsewa a ruwa, jiragen sintiri na Italiyar na kusa da su amma sai suka bar jami’an Libyan suka tafi da su, aka tsare su cikin mummunan yanayi na rashin abinci tare da dukansu har ma da yi ma wasu fyade.

Karfin hali: ‘Yan Najeriya 17 da suka tsallake nitsewa cikin kogi sun kai kasar Italiya kara (Hotuna)
Karfin hali: ‘Yan Najeriya 17 da suka tsallake nitsewa cikin kogi sun kai kasar Italiya kara (Hotuna)

gami da kuma azabtar dasu da wutar lantarki daga bisani kuma suka sayar da biyu daga cikinsu. Tuni ashirin da uku suka mutu duk kuwa daca cewa an ceto su daga karshe.

Wani Jirgin ruwan kungiyar agaji na kasar Jamani yayi nasarar ceto Mutane 59 da kuma wani jariri, kana suka kai su can kasar Italiyan.

Karfin hali: ‘Yan Najeriya 17 da suka tsallake nitsewa cikin kogi sun kai kasar Italiya kara (Hotuna)
Karfin hali: ‘Yan Najeriya 17 da suka tsallake nitsewa cikin kogi sun kai kasar Italiya kara (Hotuna)

A cikin wani gajeran bidiyo, an dai hasko yadda jami’an tsaron kan ruwan Libyan suke dukan yan ciranin, sannan suka figi jirgin nasu aguje yayin da wani ke shirin danewa a lokacin da suke yunkurin mayar da Mutane 47 zuwa Libyan.

Wannan dai shi ne karon farko da aka taba kai kasar ta Italiya kara sakamakon marawa sojojin tsaron Libyan baya.

Haka zalika an samu nasara akan Italiyan a wata shari’a da akayi a 2012 bayanda suka mikawa jami’an tsaron ruwan Libya wadansu ‘yan cirani, duk kuwa da cewa sun rigayi tsallakawa zuwa Italiyar.

Daga 2014 zuwa 2017 dai bakin haure 600,000 ne suka shiga kasar ta barauniyar hanya, amma sai dai yawansu ya ragu matuka tun bayan yarjejeniyar da suka cimma tsakaninsu da kasar Libyan.

Masu shigar da karar suna neman a biya su hakkin da aka tauye musu da kuma cin zarafi a matsayinsu na 'yan Adam.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel