Ku sadu da dan Najeriya da ya kera injin din mota mafi gudu a duniya
Tabbas Najeriya kasa ce da ta tara miliyoyin zakakurai da suka yi fice a dukkan fannonin rayuwa tun daga gida Najeriya har ma zuwa kasashen waje idan suka fita.
Watakila wannan ne ma ya sanya da shugaban kasar Najeriya a watan da ya shude ya bayyana matasa a matsayin ragwaye marasa aikata wani katabus, ya fuskanci kakkausan raddi daga dukkan bangarori.
Legit.ng ma a yau ta ci karo da wani matashi dan Najeriya mai suna Ndubisi Ezerioha da Allah ya nufa da kera injin din mota da ba'a taba yin irin sa ba a duniya.
Mun samu haka zalika cewa shi dai Injiniya Ndubisi Ezerioha dan asalin jihar Anambara ne dake a shiyyar kudu maso gabashin Najeriya kuma yanzu haka kamfanonin kera motoci na duniya kamar su Honda da sauransu suna rububin sa ne.
Takaitaccen tarihin sa dai ya nuna cewa ya kammala karatun sa na digiri ne a jami'ar jihar ta Anambara tun a shekarar 1989 kafin daga bisani ya fice zuwa kasar Amurka inda ya cigaba da karatun sa.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng