Budurwa ta shiga cakwakiya bayan da saurayi ya sulale ya bar ta ce a kawo mata abincin Naira 11,800 ranar farko
Tabbas soyayya tana da matukar tasiri a rayuwar 'yan adam haka zalika kuma fita kamar cin abinci tsakanin saurayi da budurwa musamman ma a wasu al'umma nada matukar tasiri a rayuwar masoya.
Saidai lamarin yazo da wani irin salo a tsakanin wata sambaleleiyar budurwa da kuma sabon saurayin ta biyo bayan fita da yayi da ita ya zuwa wajen cin abinci a wani bagire a daya daga cikin wuraren cin abincin Najeriya.
Legit.ng ta samu cewa zuwa wurin cin abincin ke da wuya ne sai budurwar ta bukaci cewa a kawo mata abincin da za ta ci wanda da aka yi lissafi aka lissafa ya kai Naira 11,800 shi kuma saurayin ya siya abunda zai ci na Naira 3,450 kacal.
Sai dai idon burwar ya fara rena fata ne bayan da Saurayin ya ce shi bai da kudi a jikin sa don haka budurwar ta biya duk abun da ta ci da kanta domin kuwa ya baro katin cirar kudin sa a gida.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng