Muhimman batutuwa 8 da ya kamata ku sani game da Marigari Isyaka Rabi'u

Muhimman batutuwa 8 da ya kamata ku sani game da Marigari Isyaka Rabi'u

A jiya ne dai muka samu mummunan labarin rasuwar fitaccen malamin nan kuma shahararren dan kasuwa na garin Kano wata Isyaka Rabi'u bayan wata doguwar rashin lafiyar da yayi fama da ita.

Kamar yadda labarai suka zo mana ya rasu ne a wata asibiti dake a birnin Landan kuma za'a yi jana'izar sa da zarar an kawo gawar sa gida.

Muhimman batutuwa 8 da ya kamata ku sani game da Marigari Isyaka Rabi'u
Muhimman batutuwa 8 da ya kamata ku sani game da Marigari Isyaka Rabi'u

Legit.ng kamar kullum yanzu ma gashi ta tattaro maku wasu muhimman bayanai da ya kamata ku sani game da marigayin.

1. Bayanan da muka samu dai sun nuna cewa an haifi fitaccen malamin a shekarar 1928.

2. Majiyar mu har ila yau ta ce ya yi karatun Alqur'ani da na litattafan adidni a birnin Kano.

3. Daga baya yaje birnin Maiduguri na jihar Borno domin karin karatu.

4. Daga bisani ya koma garin sa na Kano inda ya ci gaba da koyar da karatun Al'qur'ani da na litattafan addini.

5. Ya shiga harkokin kasuwanci gadan-gadan inda har ya kafa kamfanin Isyaka Rabiu & Sons.

6. Ya samu daukaka sosai a kasuwancin sa da kuma karatun Alqur'ani.

7. Daga baya ne aka nada shi shugaban Darikar Tijjaniyya a Najeriya

8. Yanzu haka kuma 'ya'yan sa sun gaji harkokin kasuwancin sa kuma suna cigaba da yi.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel