Bakare ya gargadi Buhari akan cewa kada ya bari wasu ‘yan bukulu su bata masa gwamnatinsa
- Jagoran kungiyar Save Nigeria Group, Tunde Bakare, a ranar Litinin ya gargadi shugaba Buhari da kada ya bari wasu da ake kira ‘yan zagon kasa su kawo masa matsala a gwamnatinsa
- Fasto Bakare ya fadawa shugaba Buhari cewa shine wanda za’a ga laifinsa ba wai wadanda mutanensa ba idan har gwamnatinsa ta kasa
- Tsohon abokin takarar shugaban kasar yace maganganu game da ‘yan zagon kasa zai iya zama tinani ne kawai da mutane keyi
Jagoran kungiyar Save Nigeria Group, Tunde Bakare, a ranar Litinin ya gargadi shugaba Buhari da kada ya bari wasu da ake kira ‘yan zagon kasa su kawo masa matsala a gwamnatinsa.
Fasto Bakare ya fadawa shugaba Buhari cewa shine wanda za’a ga laifinsa ba wai mutanensa ba idan har gwamnatinsa ta kasa, ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da Channels Television game da zaben 2019.
Tsohon abokin takarar shugaban kasar yace maganganu game da ‘yan zagon kasa zai iya zama tinani ne kawai da mutane keyi, yace Buharin da ya sani yana yin abunda yaso musamman idan ya sawa ransa.
Bakare yace duk da mutane na maganganu game da shugaba Buhari suna cewa ya cika nawa a mulkinsa game da yanke shawarwari, kuma mulki yanason hanzari a cikinsa , yace yana duba abu kafin ya yanke hukunci akansa.
KU KARANTA KUMA: Buhari kadai keda damar bayyana lafiyarsa - Adesina
Bayan haka ya shawarci shugaba Buhari da ya ringa bayyana kurakurai na mulkinsa a kokarin da yakeyi na mulkin adalci ga jama’ar Najeriya
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng