Hadakar fatattakar Buhari ta Obasanjo ta yi wa Buhari wankin babban bargo

Hadakar fatattakar Buhari ta Obasanjo ta yi wa Buhari wankin babban bargo

Hadakar nan ta wasu zaratan 'yan Najeriya da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya assasa da zummar maido da martabar kasar a bisa turba daidaitacciya watau Coalition for Nigeria Movement (CNM) ta yi wa shugaba Buhari wankin babban bargo.

Hadakar ta Coalition for Nigeria Movement dai kamar yadda muka samu ta na maida martani ne ga shugaban kasar game da kalaman sa a yayin wata fira da yayi lokacin ziyarar sa kasar Amurka game da yadda tsaffin shugabannin kasar Najeriya suka lalata kasar.

Hadakar fatattakar Buhari ta Obasanjo ta yi wa Buhari wankin babban bargo
Hadakar fatattakar Buhari ta Obasanjo ta yi wa Buhari wankin babban bargo

Legit.ng ta samu cewa hadakar ta CNM ta bayyana takaicin ta ne a kan yadda shugaban a duk inda ya bode baki baya yabon kowa sai kan sa.

A wani labarin kuma, Dan majalisar tarayya a zauren majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kagarko/Kachia mai suna Honorable Jagaba Adams Jagaba ya sanar da ficewar sa daga jam'iyyar APC zuwa jam'iyyar adawa a jihar ta PDP.

Dan majalisar ya sanar da hakan ne a lokacin da aka shirya masa gangamin tarba a ranar Litinin din da ta gabata a garin Zonkwa ta Zangon Kataf tare da dumbin magoya bayan sa da suka kai mutum 4,556.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel