Aiki sai Maza: Dakarun Sojojin Najeriya sun yi nasarar kuɓutar da sama da Mutane Dubu daga hannun ƴan Boko Haram
- Sojoji na cigaba da samun nasara a cigaba da yaki da yan ta'addan Boko Haram
- A wannan karon, sojojin sunyi nasarar kubutar da Mutane sama da 1,000
- Sun kubutar da wadanda yan Boko Haram din suka kame ne a jihar Borno
Rundunar Sojin kasar nan ta bayyana cewa ta yi nasarar kubutar da mutane sama da 1,000 daga hannun 'yan tada kayar baya na Boko Haram a wasu kauyuka dake karamar hukumar Bama a jihar Borno.
Kakakin rundunar sojin Bri. Gen. Texas Chukwu ne, ya bayyana hakan a ranar litinin. Chukwu ya ce an gudanar da wannan ceton bisa jagoranci tawagar 22 Brigade karkashin atisayen lafiya dole wanda ya samu hadin gwuiwa da Multinational Joint Task Force (MNJTF).
Ya lissafo jerin kauyukan da aka yi nasarar ceton wadannan mutane daga cikinsu wadanda suka hada da; Malamkari, Amchaka, Walasa da kuma kauyen Gora wanda duk suke karkashin karamar hukumar Bama dake Jihar Borno.
KU KARANTA: Inda ranka: Yamutsi bayan da gwaggwon biri ya biyo wani manomi har gida a jihar Kuros
Ya kara da cewa, yawancin wadanda aka yi nasarar cetowar mata ne da kuma kananan yara sai kuma matasa, wanda da yawansu an tilasta su ne da su zama mayakan na Boko Haram ba bisa san ransu ba.
Chukwu, ya bayyanawa jama'a cewa rundunar sojin tana cigaba da jajircewa domin ganin ta kawo karshen Boko Haram baki daya. Har wa yau ya umarci jama'a da su cigaba da bawa jami'an tsaro hadin kai wajen bada bayanai ga duk wani abu da basu yadda da shi ba ga jami'an tsaro mafi kusa dasu.
Yanzu haka dai wanda aka ceton suna can ana cigaba da duba lafiyarsu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng