Buhari ya ziyarci fadar Sarkin Katsina don yin ta’aziyyar rasuwar babban Limamin masallacin jihar

Buhari ya ziyarci fadar Sarkin Katsina don yin ta’aziyyar rasuwar babban Limamin masallacin jihar

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin, ya ziyarci Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumuni Kabir Usman, bisa ga rasuwar babban limamin masalacin jihar Katsina, Liman Lawal

- Babban Limamin ya rasu ne a ranar Lahadi da safe, ya rasune yana da shekaru 95 kuma ya bar mata hudu da yara ashirin da bakwai

- Anyi zana’idarsa da rana, wanda Gwamnan jihar Katsina Aminu Masari da Sarkin Katsina suna cikin wadanda suka halarci zana’idar tare da sauran manyan mutanen jihar

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin, ya ziyarci Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumuni Kabir Usman, bisa ga rasuwar babban limamin masalacin jihar Katsina, Liman Lawal.

Babban Limamin ya rasu ne a ranar Lahadi da safe, ya rasune yana da shekaru 95 kuma ya bar mata hudu da yara ashirin da bakwai.

Anyi zana’idarsa da rana, wanda Gwamnan jihar Katsina Aminu Masari da Sarkin Katsina suna cikin wadanda suka halarci zana’idar tare da sauran manyan mutanen jihar, tare da dumbin mutanen jihar Katsina a zana’idar da aka gudanar a gaban gidan Sarkin Katsina.

Shugaba Buhari ya isa fadar Sarkin bayan karfe goma da mintina kadan na safe, kuma ya tafi bayan mintina talatin.

KU KARANTA KUMA: Sojoji sun ganawa wani mai cutar asthma da dan uwansa azaba a jihar Legas

Gwamnan jihar Katsina Aminu Masari shine wanda ya raka shugaban kasar tare da mataimakinsa Alhaji Mannir Yakubu, da kuma Sakataren gwamnatin jihar Katsina Dr. Mustapha Inuwa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng