Yanzu-yanzu: Kuma dai, kotu ta hana beli Sanata Dino Melaye
Alkalin alkalan babban kotun jihar Kogi Jastis Nasiru Ajanah ya dakatad da karar sauraron belin sanata mai wakiltar Kogi ta yamma a majalisar dattawa, Sanata Dino Melaye
Jastis Nasiru Ajanah ya dakatad da karan ne zuwa ranan Alhamis, 10 ga watan Mayu, 2018.
Ya ce ya yanke hakan ne saboda lauyoyin hukumar yan sanda da na Dino Melaye basu shigar da ranstuwa kan neman belin ba.
Sanatan dai a yanzu yana kwance a babban asibitin tarayya da ke Abuja kuma karkashin kulawan hukumar yan sandan Najeriya bayan gurfana da yayi a kotun majistare da ke Lokoja.
Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa Sanata mai wakiltan mazabar Kogi ta Yamma a majalisan dattawan Najeriya, Dino Melaye, a ranan Litinin ya bayyana cewa ya tsallo daga motan yan sandan ne saboda sau biyu suna watsa masa barkonon tsohuwa a cikin mota.
Sanatan a wani karar da lauyansa, Mike Ozekhome, ya shigar babban kotun Lokoja ya ce ya fado ne kuma saboda yan sandan sunyi alkawarin gurfanar da shi gaban babban kotun birnin tarayya.
Amma, alkalin alkalan jihar Kogi, Jastis Nasir Ajana, ya dakatad da karan zuwa ranan Alhamis domin dubi cikin neman belin da sanatan yayi.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng