Zaku iya gane yan kunar bakin wake ta yanayin shigar su - Buratai

Zaku iya gane yan kunar bakin wake ta yanayin shigar su - Buratai

- Tukur Buratai, shugaban hafsan soji, ya bayar da alamomi na yadda za’a gane masu kunar bakin wake, lokacin da ya kai ziyara a garin Mubi

- Buratai ya bayyana cewa an samu cigaba ta fannin tsaro sosai dangane da yanda yanayin tsaron yake a shekaru uku da suka gabata

- Sarkin Mubi, Abubakar Ahmadu, ya bayyana cewa ofishin sarkin tare da jami’an tsaro sun bayyana matsalolin da ake samu ta fannin tsaro wadanda ya kaiga ‘yan kunar bakin wake suka samu shiga cikin garin

Tukur Buratai, shugaban hafsan soji, ya bayar da alamomi na yadda za’a gane masu kunar bakin wake, lokacin da ya kai ziyara a garin Mubi a satin da ya gabata, a jihar Adamawa.

Buratai ya bayyana cewa an samu cigaba ta fannin tsaro sosai dangane da yanda yanayin tsaron yake a shekaru uku da suka gabata.

Buratai ya kara da cewa za’a iya gano yan kunar bakin wake ta yanayin shigarsu, domin suna yin shiga ne ba na lafiya ba, don haka ya zama dole a dunga kula.

Zaku iya gane yan kunar bakin wake ta hanyar shigar su - Buratai
Zaku iya gane yan kunar bakin wake ta hanyar shigar su - Buratai

Sarkin Mubi, Abubakar Ahmadu, ya bayyana cewa ofishin sarkin tare da jami’an tsaro sun bayyana matsalolin da ake samu ta fannin tsaro wadanda ya kaiga ‘yan kunar bakin wake suka samu shiga cikin garin.

KU KARANTA KUMA: Sojoji sun ganawa wani mai cutar asthma da dan uwansa azaba a jihar Legas

Ahmadu yace sama da mutane 20 suka mutu a harin da aka kai, sai kuma wasu 50 sun samu raunuka a bamabaman da suka tashi a wurare daban daban a ranar 1 ga watan Mayu, a garin Mubi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng