Kwankwaso da mataimakin gwamnan jihar kano sun zagayewa zaben APC
- Biyu daga cikin manyan jagororin APC a jihar Kano sun zagayewa zaben jam’iyyar wanda aka gudanar a ranar Asabar
- Tsohon gwamnan jihar kano kuma sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya, Rabiu Kwankwaso, da kuma mataimakin gwamnan jihar Kano, Hafiz Abubakar, sun zagayewa zaben APC, wanda aka gudanar a ranar Asabar
- Zaben da aka gudanar a Madobi, karamar hukumarsu Kwankwaso, wanda kwamishinan cigaban birane da kauyuka ya kula dashi, Musa kwankwaso, kuma a matsayinsa na abokin adawar Rabiu kwankwaso a siyasa
Biyu daga cikin manyan jagororin APC a jihar Kano sun zagayewa zaben jam’iyyar wanda aka gudanar a ranar Asabar.
Tsohon gwamnan jihar kano kuma sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya, Rabiu Kwankwaso, da kuma mataimakin gwamnan jihar Kano, Hafiz Abubakar, sun zagayewa zaben APC, wanda aka gudanar a ranar Asabar.
Zaben da aka gudanar a Madobi, karamar hukumarsu Kwankwaso, wanda kwamishinan cigaban birane da kauyuka ya kula dashi, Musa kwankwaso, kuma a matsayinsa na abokin adawar Rabiu kwankwaso a siyasa.
KU KARANTA KUMA: Abunda Buhari ya fada mani dangane da taron APC na kasa - Okorocha
Tsohuwar mai bawa tsohon gwamnan shawara ta fannin sadarwa Binta Sipikin, ta bayyanawa Premium Times cewa, mambobin APC magoya bayan Kwankwaso, sun gudanar da zabensu daban a mazabobi 484 na jihar Kano.
A halin da ake ciki, Okorocha ya bayyanawa manema Labarai, cewa ya sanar da shugaban kasar yadda tarurrukan jam’iyyar ta APC ta gudana a fadin kasar, inda ya bayyana rashin jin dadinsa game da yadda wasu ‘yan jam’iyyar suka nuna wata halayya a lokacin taron.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng