Uwa ta siyar da jaririnta a kan kudi N300,000 shi kuma wanda ya siya ya sake siyar dashi akan N350,000
- Wata uwa mai zaman kanta, Ezechi Nwanneka, ta shiga hannun hukuma a jihar Enugu, sakamakon siyar da jaririnta da tayi akan kudi N300,000
- Yaron wanda aka gano, an siyar dashi ne akan kudi N350,000, a hannun Okechukwu Nyia, wanda ya siya jaririn daga hannun Nwenneka ita mahaifiyar
- Nwanneka ‘yar kauyen Akama Oghe, a karamar hukumar Ezeagu, wadda ba’a san wanda yayi mata cikin ba
Wata uwa mai zaman kanta, Ezechi Nwanneka, ta shiga hannun hukuma a jihar Enugu, sakamakon siyar da jaririnta da tayi akan kudi N300,000.
Yaron wanda aka gano, an siyar dashi ne akan kudi N350,000, a hannun Okechukwu Nyia, wanda ya siya jaririn daga hannun Nwenneka ita mahaifiyar jaririn.
Nwanneka ‘yar kauyen Akama Oghe, a karamar hukumar Ezeagu, wadda ba’a san wanda yayi mata cikin ba, a jihar Enugu.
Labara yazo cewa a watan Nuwamba na 2017, ta bar gida zuwa wani wuri da ba wanda ya san ko ina ne, amma dai ta bayyana cewa ta haifi jariri namiji, amma dai bata nunawa danginta jaririn ba, wanda suka shiga zargi a lokacin da ta dawo gida babu jaririn.
Iyayen Nwanneka ne suka sanar da hukumar ‘Yan Sanda, suka binciko cewa ta siyarwa Nyia da jaririn akan kudi N300,000.
KU KARANTA KUMA: Hanyoyi 5 dake hana furfura fitowa a jikin mutum
Mai magana da yawun hukumar ‘Yan Sandan na jihar Enugu, Mr. Ebere Amariazu, ya tabbatar da cigaban da aka samu sakamakon bincike, inda ya bayyana cewa zasu cigaba da bincike har sai sun gano wada aka siyarwa da jaririn.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng