Harin Birnin Gwari: 'Yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutane 45

Harin Birnin Gwari: 'Yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutane 45

- Hare-haren yan bindiga ya bar kauyen Gwaska cikin jimami da sallami

- Harin baya-bayan da 'yan bindiga suka kai a birnin gwari dake jihar Kaduna yayi sanadiyyar mutuwar mutanen da har ya zuwa yanzu ba'a gama gano adadinsu ba

A kalla gawar Mutane 45 aka gano a sakamakon harin da 'yan bindiga suka kai kauyen Gwaska dake karamar hukumar Birnin-Gwari ta jihar Kaduna.

Harin Birnin Gwari: 'Yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutane 45
Harin Birnin Gwari: 'Yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutane 45

Majiyarmu dai ta rawaito cewa, mazauna kauyen da yawansu ya kai kimanin 500 tare da taimakon yan sintiri na yankin da kuma taimakon Sojoji ne suka kwashe gawarwakin da yammacin yau Lahadi.

KU KARANTA: Sabon salo: Dole ne kowanne 'Dan sanda da za'a dauka ya rubuta JAMB

"Abinda muka sani shi ne, gawa 12 aka dauke jiya asabar, sannan kuma yanzu ga 33 an kawo fadar sarki Birnin Gwari, hakan ya nuna cewa gawarwaki 45 kenan. Amma babu tabbacin ko harin na ramuwar gayya ne, kasancewar bincike ya nuna cewa, akwai tsattsamar dangantaka tsakanin yan kauyen Gwaskan da wasu yan bindiga." A cewar Kwamishinan 'Yan sanda na yanki. Kana ya kara da cewa, sun tura jami'ai domin kare faruwar hakan a gaba.

Wani mazaunin yankin Aminu Abubakar, ya tabbatar dsa cewa. gawarwakin dai da fari an ajiye su ne a fadar Sarkin Birnin Gwari don sallatarsu kafin daga bisani a tafi da su izuwa garin

Doka domin jana'iza. Kuma jami'an tsaro basu yarda an je kusa ko daukar hoton gawarwakin ba.

Amma sai dai wani mazaunin yankin ya ce, da akwai yiwuwar kara samun wasu gawarwakin domin yanzu haka ana cigaba da bincike a cikin daji.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel