Sabon salo: Dole ne kowanne 'Dan sanda da za'a dauka ya rubuta JAMB

Sabon salo: Dole ne kowanne 'Dan sanda da za'a dauka ya rubuta JAMB

- Duk masu shirin neman aikin 'Dan sanda sai sun zage damtse a wannan karon, sakamakon sabbin tsare-tsaren da aka fito da su

- Kuma Babban Sufeton 'Yan sanda na kasa ya umarci da'a saka ido wajen gani an dauki wadanda suka cancanta ba tare da alfarma ba

Babban Sufeton 'Yan sanda na kasa IGP Ibrahim K. Idris NPM, mni, ya bayyana cewa, sabbin jami'an da za'a dauka dole sai sun rubuta jarrabawar tantancewa ta JAMB kafin daukar tasu. Ya bayyana hakan ne ta bakin kakakin rundunar kasa ACP, Jimoh Moshood.

Sabon salo: Dole ne kowanne 'Dan sanda da za'a dauka ya rubuta JAMB
Sabon salo: Dole ne kowanne 'Dan sanda da za'a dauka ya rubuta JAMB

A cewar rundunar, wannan wani yunkuri ne na tabbatar da sahihanci da kuma tsantseni wajen daukar duk wadanda suke son zama jami'an 'Yan sandan da za'a fara daga gobe 7 ga watan Mayu.

Babban Sufeton IGP Ibrahim K. Idris, ya kuma gargadi dukkannin jami'an rundunar na jahohi 36 tare da birnin tarayya Abuja da su kasance sun bi dokokin da aka sanya wajen tantance wadanda za'a dauka aikin na 'Dan sanda.

Ibrahim K. Idris yayin da yake jawabi ga manyan jami'an 'Yan sanda ta hannun mataimakinsa DIG Emmanuel Inyang, yayi kira gare su da su tabbatar da cewa an bi doka wajen fara tantancewar a gobe Litinin. Sannan ya kuma gargade su da su cire son kai yayin tantancewar.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari ta amince a saki Biliyan 80 domin hanyar Legas zuwa Ibadan

Sai dai wani sabon salo da rundunar ta bullo da shi na batun zana jarrabawar JAMB kafin samun shiga aikin, wanda hakan na a matsayin karon farko da ta faru a runduna.

Bayan tantancewar lafiyar jiki yanzu masu neman aikin zasu gudanar da jarrabawar rubutu da JAMB zata shirya domin tabbatar da an dauki wadanda suka cancanta.

Sannan kuma za'a gwada lafiyar kowannensu, da tantance karfin gani daga nesa da na kusa da bambance launin kaloli da kuma gwajin karfin jin kunne da gwajin ciwon tarin fuka da ciwon siga da hawan jini da cuta mai karya garkuwar jiki da kuma gwajin juna biyu ga mata.

Daga nan ne kuma za'a gudanar da tantancewar karfin zurfin tunani da dabi'a da kuma gwajin shaye-shaye kwayoyi.

Sabon salo: Dole ne kowanne 'Dan sanda da za'a dauka ya rubuta JAMB
Sabon salo: Dole ne kowanne 'Dan sanda da za'a dauka ya rubuta JAMB

Babban Sufeton ya kuma umarci mataimakin nasa da ya tabbatar da cewa sun sanya idanu a yayin tantancewar don tababtar da an gudanar da ita yadda ya kamata a duk fadin jahohin Najeriya da kuma Abuja.

Haka zalika, an shawarci iyaye da masu neman aikin na 'Dan sanda da su kai korafinsu yayin da suka ga wani abu na dai-dai ba ga lambobin wayar da suka bayar.

08076036011, 08037036257, 08034360919, 08037855951, 08065823054, 08036753589. A sanarwar da kakakin rundunar ACP, Jimoh Moshood ya sanyawa hannu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel