An shirya magabta biyu na siyasar jihar Borno bayan Ali ya dawo APC

An shirya magabta biyu na siyasar jihar Borno bayan Ali ya dawo APC

- Ali Modu ya bata da gwamna da ya nada a jiharsa ta Borno a 2011

- Yaje PDP amma sam lamarin bayyi masa dadi ba

- A yanzu Ali Modu ya gudu daga PDP ya koma cikin abokansa na ANPP

An shirya magabta biyu na siyasar jihar Borno bayan Ali ya dawo APC
An shirya magabta biyu na siyasar jihar Borno bayan Ali ya dawo APC

Jijjige guda a jihar Borno, Sanata Maliya, Ali Modu Sheriff, wanda ya mulki jihar a 2003-2011, ya kai gwauro ya kai mari yaga babu maita illa ya koma cikin jam'iyyarsa ta APC bayan da PDP tayi watsi dashi a matsayin shugaba.

Ya dai wahalar da PDPn inda aka shafe shekaru a kotu kan ko waye uban tafiyar PDPn a wancan lokaci bayan ta fadi zabe.

Yayi ta watsin kudi a titunan Borno a ranar juma'ar nan, inda suke ta ihu suna bin motocinsa da Yirne! Yirne! Yirne! watau watso! watsi! watso! da yarensu na Kanuri. LAvarin komawarsa APC ta baiwa jama'a mamaki da nishadi.

DUBA WANNAN: An gano Boko Haram na sallar gawa kafin hare-hare

An gana da gwamna Shettima, wanda a da basu ga-maciji da Sanatan kuma tsohon gwamna da ya nada shi a 2011 a gidan gwamnati, bayan an kori manema labarai.

Ba'a san ko yana so ya dora wani a gwamna bane a jihar, ko kuma tsoron kar jihar ta kubuce masa kacokan bayan gwamnan shimma ya dora nasa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel