Zaben 2019: Jam'iyyar PDP ta kaddamar da kwamitin tuntuba da 'maja'

Zaben 2019: Jam'iyyar PDP ta kaddamar da kwamitin tuntuba da 'maja'

Jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party, PDP a matakin kasa baki daya a ranar Juma'ar da ta gabata ne dai ta kaddamar da wani muhimmin kwamitin da zai jagoranci kwace mulki daga hannun APC a zabukan 2019 masu zuwa.

Shuganan jam'iyyar na kasa ne dai Prince Uche Secondus ya kaddamar da kwamitin a babbar Sakatariyar jam'iyyar dake a garin Abuja yana mai cewa ya zama dole jam'iyyar ta kafa kwamitin.

Zaben 2019: Jam'iyyar PDP ta kaddamar da kwamitin tuntuba da 'maja'
Zaben 2019: Jam'iyyar PDP ta kaddamar da kwamitin tuntuba da 'maja'

KU KARANTA: Yan bindiga sun kashe mutane 13 a Zamfara

Legit.ng ta samu cewa shima da yake jawabi a madadin sauran 'yan kwamitin, shugaban kwamitin da ke kuma ke zaman tsohon gwamnan Ribas Lyal Imoke ya bayyana cewa za su yi aiki tukuru domin ganin sun samu nasara.

A wani labarin kuma, Labarin da muke samu da dumin sa daga kafofin yada labaran mu na nuni ne da cewa kwamitin da ke da alhakin gudanar da zabukan shugabannin jam'iyya mai mulki a jihar ta APC karkashin jagorancin Musa Mahmud ya dage yin zaben har sai zuwa ranar Lahadi mai zuwa.

Musa Mahmud, kamar yadda muka samu ya sanar da hakan ne jim kadan bayan kammala tattaunawa da jiga-jigai da kuma masu ruwa da tsaki na jam'iyyar bisa dalilin cewar har yanzu akwai wasu da ba su samu damar sayen fom din su ba.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel