Da dumin sa: Jam'iyyar APC a jihar Adamawa ta soke yin zaben shugabannin mazabun ta

Da dumin sa: Jam'iyyar APC a jihar Adamawa ta soke yin zaben shugabannin mazabun ta

Labarin da muke samu da dumin sa daga kafofin yada labaran mu na nuni ne da cewa kwamitin da ke da alhakin gudanar da zabukan shugabannin jam'iyya mai mulki a jihar ta APC karkashin jagorancin Musa Mahmud ya dage yin zaben har sai zuwa ranar Lahadi mai zuwa.

Musa Mahmud, kamar yadda muka samu ya sanar da hakan ne jim kadan bayan kammala tattaunawa da jiga-jigai da kuma masu ruwa da tsaki na jam'iyyar bisa dalilin cewar har yanzu akwai wasu da ba su samu damar sayen fom din su ba.

Da dumin sa: Jam'iyyar APC a jihar Adamawa ta soke yin zaben shugabannin mazabun ta
Da dumin sa: Jam'iyyar APC a jihar Adamawa ta soke yin zaben shugabannin mazabun ta

Legit.ng ta samu cewa wasu daga cikin wadanda suka yi korafin rashin isasshen lokacin siyen fom din takarar sun hada da Babachir Lawal, Abdulaziz Nyako, Abubakar MoAllayidi, Nuhu Ribadu da kuma Marcus Gundiri.

A wani labarin kuma, Wata kotun daukaka kara ta gwamnatin tarayya dake zaman ta a garin Legas ta yanke hukuncin cewa yanzu gwamnatin tarayya na da hurumin mika Sanata Buruji Kashamu dake wakiltar jihar Ogun ta gabas zuwa kasar Amurka bisa zargin fataucin miyagun kwayoyi.

Wannan hukuncin da kotun ta yanke na matsayin yin fatali ne da wani hukunci da karamar kotu ta yanke game da batun na hana gwamnatin tarayyar ta kai shi.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng